APCn Kano sai tsiyayewa ta ke yi, ƴan majalisa uku sun koma Jam’iyya mai alamar kayan maimari, NNPP

‘Yan majalisan dokokin jihar Kano uku sun tuma tsalle daga jami’iyyar APC sun tsunduma jam’iyyar NNPP mai alamar kayan marmari.
Kakakin majalisar Uba Abdullahi ya sanar da haka yana mai cewa ‘yan majalisar sun sanar da sauya shekar ne a wasikun da suka aika wa kakakin majalisar.
Yan majalisan da suka canja sheka sun hada da Abdullahi Iliyasu Yaryasa Mai wakiltar Tudun Wada, Muhammad Bello Butu Butu Mai wakiltar Tofa/Rimin Gado da Kabiru Yusuf Ismaila na Madobi.
Idan ba a manta ba PREMIUMTIMES ta buga labarin yadda ‘yan majalisan Kano 9 da aka zabe su a karkashin jam’iyyan PDP suka canja sheka zuwa jami’yyar NNPP.
‘Yan majalisan sun ce sun yi haka ne saboda matsalolin shugabanci da Jam’iyyar PDP ke fama da shi a ƙasar nan.
Wadannan ƴan majalisar sun haɗa da Isyaku Ali Danja Mai wakiltar Gezawa, Umar Musa Gama mai wakiltar Nassarawa, Aminu Sa’adu Ungogo mai wakiltar Ungogo, Lawan Hussain Chediyar ‘Yan Gurasa mai wakiltar Dala da Tukur Muhammad mai wakiltar Fagge.
Saura sun hada da Mu’azzam El-Yakub mai wakiltan Dawakin Kudu, Garba Shehu Fammar mai wakiltar Kibiya, Abubakar Uba Galadima mai wakiltar Bebeji da Mudassir Ibrahim Zawaciki mai wakiltan mazabar Kumbotso.
A ranar 29 ga Afrilu majalisar ta sanar cewa Salisu Gwangwazo dake wakiltar Kano Municipal a karkashin inuwar jami’ayya PDP ya koma jami’iyyar APC.