An koro ƴan wasan Najeriya 10 daga Wasannin Olamfik a Japan, dalilin kauce wa gwajin amfani da ƙwayoyin a-ji-garau

Ƙoƙarin da Najeriya ke yi don ganin ta ciwo gwala-gwalai da azurfa da tugulla a Gasar Wasannin Olamfik da ake yi a Tokyo, ya haɗu babbar tangarɗa, sakamakon koro wasu ‘yan wasan Najeriya 10 da aka yi.

‘Yan wasan 10 na Najeriya na cikin ‘yan wasa 18 da Hukumar Tantancewa da Gwajin Jinin ‘Yan Wasan Olamfik ta ce ba su cancanci su shiga gasar ba.

Hukumar ta ce ba su cika sharuɗɗa adadin gwajin jinin da Doka ta 15 ta ce kowane ‘yan wasa na wasu kaɓantattun ƙasashe su cika.

Hukumar Gwaji ta AIU ta gindaya cewa Dokar Haramta Amfani da Kwayoyi Domin Ƙara Kuzari (Anti-Doping Obligations), wadda aka ƙirƙiro a cikin watan Janairu, 2019, ta na da haƙƙin tabbatar da cewa an bi ƙa’ida tilas ‘yan wasa sun gwaje-gwaje guda ukun da aka ce su yi kafin lokacin fara gasar Olamfik ta zo.

Sauran sharuɗɗan sun haɗa da:

1. Duk ƙasashen da Hukumar Olamfik ta jera a rukunin “A”, to su ne za su fi fuskantar zargi, kuma za a fi umarnin ƙasashen su riƙa yi wa ‘yan wasan gwajin amfani da ƙwayoyin a-ji-garau.

2. Doka ta 15 ta gindaya cewa tilas ɗan wasan da ke cikin ƙasashen rukuni na “A”, sai an yi masa gwajin jini sau uku. Kuma ba sai an sanar da shi ranar da za a yi masa ba. Sai dai a yi masa taso mu je a gwada ka. Kuma ba zai ce ku jira sai na shirya ba.

3. Za a gwada jinin ɗan wasa ne da fitsarin sa, domin a gane ko ya sha wata ƙwaya ko kafson ƙara masa kuzari a wajen guje-guje da tsalle-tsalle.

4. Zai kasance an yi gwaje-gwajen uku bayan kowane mako uku, a cikin watanni 10 kafin ranar fara Gasar Olamfik.

5. Sai ‘yan wasan da su ka cika waɗannan sharuɗɗan ne za su cancanci shiga wata Gasar Guje-guje da Tsalle-tsalle ta Duniya, ciki har da Gasar Olamfik.

6. A shekarar 2021, an ɗora ƙasashe 7 a “Rukunin A”. Daga cikin su akwai Najeriya, Belarus, Bahrain, Ethiopia, Kenya, Morocco da Ukraine.

Wanda Bai Ji Bari Ba Zai Ji Hoho: Yadda Hukumar Shirya Wasanni ta Najeriya Ta Janyo Korar ‘Yan Najeriya Daga Olamfik A Tokyo:

Kusan tsawon watanni 14 Hukumar Kula da Wasanni ta Kasa, AFN ta shafe ta na rikici na babu gaira babu dalili.

Hukumar Olamfik ta jefa sunan Najeriya cikin ƙasashen “Rukunin A” a farkon 2020, saboda an lura ba ta dauki batun gwajin jinin ‘yan wasan ta da muhimmanci ba.