Yadda jami’an tsaro suka kama ƙasurgumin ɗan bindiga a shagon siyar da maganin kara karfin maza

Kakakin rundunar Sibul Difens Hamza Illela ya bayyana yadda jami’an rundunar suka damƙe wani ƙasurgumin ɗan bingan Bello Galadima a Sokoto.

Illela ya ce a ranar Talata jami’an rundunar suka yi wa wa Bello diran bazata a Unguwar Hamma Ali a wani shagon saida magani ya na siyan maganin ƙara ƙarfin maza.

Kwamandan rundunar ya yabawa mutanen gundumar Hamman Ali kan bayanan sirri da suka baiwa jami’an tsaron.