An kashe mutum biyar a hatsaniyar siyasa a Gombe

Raba a Facebook

Tura zuwa Twitter

Gwamnatin Jihar Gombe ta yi Allah-wadai da hatsaniyar da ta faru a babban birnin jihar, yayin ziyarar da tsohon gwamnan jihar kuma Sanata mai wakiltar Gombe ta tsakiya Sanata Danjuma Goje ya kai Gombe.

Cikin wata sanarwa da Kwamishinan yaɗa labarai na jihar Julius Ishaya Lepes ya fitar ya ce Goje ya tattaro ‘yan daba daga kananan hukumomin jihar daban-daban ɗauke da makamai domin su raka shi inda zai je daga filin jirgin saman da ya sauƙa.

Sanarwar ta ƙara da cewa ko a bara lokacin babbar sallah yaran Sanata Goje sun tayar da hayaniyar da kuma ta yi sanadin mutuwar mutum biyu a lokacin.

  • Facebook

    Twitter

Labarin baya“Matasa ku guji karbar aiki a ƙarshen gwamnatin Ganduje” Mu’azu Magaji

Hausa Daily Times ingantacciyar kafar yaɗa labarai ce da ke da ƙwararrun ma’akata ƙarƙashin jagorancin ƙwararrun ƴan jarida.