An ji ƙaran fashewan wani abu kamar Bom a Kaduna

Raba a Facebook

Tura zuwa Twitter

Wasu yara uku sun raunana bisa fashewar wani abu mai ƙara da ya faru a yammacin yau Asabar a Kaduna.

Lamarin ya faru ne a unguwar Badarawa dake birnin Kaduna, inda aka ce ɗaya daga cikin yaran da suka jikkata, hannayensa sun yanke.

Daily Trust ta ruwaito lamarin ya faru ne lokacin da yaran suke wasa da gorunan lemo da wani ya basu.

Yayin da biyu daga cikin yaran da abin ya rutsa da su likitoci ke ƙoƙarin ceto rayuwarsu a asibiti, an bayyana cewa hannayen ɗaya daga cikinsu nan take suka guntule.

“Lamarin gaskiya na hankali ne saboda nan take hannayen ɗaya daga cikin yara sun yanke sannan fashewan ya shafi idanunsa ɗaya, shi kuma ɗayan yaron ya samu mummunan rauni.”

“Na ukun dai da sauƙi domin shi bai samu mummunan rauni sossai ba. Sun ce wani ne ya basu gorunan Bobo su yi wasa da su”. A cewar wata majiya.

Ƙarin bayani na nan tafe

Cikakkun bayanai daga baya…