ALLURA CIKIN RUWA: Wa APC Za Ta Zaba Don Zama Shugaban Jam’iyya A Katsina? Daga Muhammad Bello

Ganin watanni shida da uwar jam’iyyar APC ta tsara domin shirya taron jam’iyyar da za’a zabi shugabannin a kowane matakai ya na ƙara matsowa, kusan saura kwanaki ƙalilan. An fara hasashen su wa za su zama shugabannin jam’iyar a matakan ƙasa da jihohi da shiyyoyi da ƙananan hukumomi da kuma gundumomi a duk faɗin ƙasa.

Duk da wasu na ganin kwamitin riƙon na ƙasa bai shirya gudanar da wannan taron ƙasa ba, wasu ma har sun fara yamaɗiɗin cewa shugabancin na Gwamna Mai Mala Buni za su ƙara neman wa’adin, kamar zuwa yanzu ba su shirya gudanar da zaben ba. Saboda zuwa yanzu ya kamata a ce sun fitar da yadda jaddawalin zabe da kuma sharuɗɗan tsayawa takara a matakai daban-daban.

A Jihar Katsina ma an fara hasashen waɗanda za su tsaya takarar muƙamai sama da ashirin da za’a cike guraben su. Wasu daga cikin masu son sha’awar tsayawa wa takara sun fara tuntuba ta ƙarƙashin ƙasa, wasu kuma suna tuntubar iyayen gidan su yadda za’a bullo wa tsayawa takarar muƙamai daban-daban. Abin da mutanen Jihar Katsina ke tambaya shi ne, shin Gwamna ko Gwamnatin Jiha na da wanda ta tsaida? Shin za’a yi karba-karba tsakanin shiyyoyin Katsina da Daura da kuma Funtua saboda yanzu ɗan shiyyar Katsina ke yi? Mataimakin Gwamna Mannir Yakubu da Sakataren Gwamnatin Jihar Katsina, ana kallon kamar su na da sha’awar tsayawa takarar gwamna.

Shin kowane daga cikin su zai tsaida ɗan takara?

Aƙalla wakilan jamiyyar 4,814 daga matakai daban-daban ne ake sa ran za su jefa ƙuri’a a matakin shugabancin jam’iyyar APC a Jihar Katsina. Akwai muƙamai a matakin jiha har guda 20, waɗanda za’a zaba, domin tafiyar da jamiyyar a matakin jiha.

Kamar yadda kowa ya sani, uwar jam’iyyar APC a matakin ƙasa ta rushe kafatanin shugabancin jam’iyyar a matakan ƙasa da jihohi da ƙananan hukumomi a duk faɗin ƙasar nan.

Wannan ya bai wa Shugaban Jam’iyyar a Jihar Katsina, Malam Shitu S. Shitu damar ci gaba da tafiyar da jam’iyyar tare da kwamitin zartaswa na jam’iyyar na jiha da na shiyya. Haka kuma Shugaban Rikon jam’iyyar na jiha, Malam Shitu ya rantsar da shugabannin jam’iyyar na rikon a helkwatar jam’iyyar ta jiha a matakin ƙananan hukumomi talatin da huɗu na jihar Katsina su ma su tafi su ci gaba da jan ragamar jam’iyyar, kamar yadda uwar jam’iyyar ta ƙasa ta umurta.

A halin da ake ciki yanzu dai jam’iyyar APC ba ta da zababbun shugabannin jam’iyya a kowane matakai, sai da shugabannin riƙo kafin a fiddo da jaddawalin zaben. A jihar Katsina akwai muƙamai sama da guda 20, wanda tuni wasu daga cikin masu rikon kwaryar jam’iyyar a matakai daban-daban sun fara nuna sha’awar su ta tsayawa takarar shugabancin jam’iyyar APC mai mulki a ƙasar nan dama jihar Katsina, inda nan ne mahaifar Shugaba Muhammadu Buhari.

A jihar Katsina dai, yanzu kallo ya fara komawa sama, watau ga wa zai shugabanci jam’iyyar APC a jihar? Kuma su wa su ka fara nuna sha’awar tsayawa takarar? Shin jam’iyyar APC za ta yi karba-karba ne ganin Gwamna ya fito daga shiyyar Funtua, shi kuma shugaban jam’iyyar ya fito daga shiyyar Katsina? Ko kuwa duk mai sha’awar tsayawa takarar shugabancin ya na iya tsayawa ba tare da la’akari da shiyyar da ya fito ba? Shin ko za a duba yiwuwar inda za’a fitar da dan takarar gwamna a zaben 2023? Me ya sa har yanzu masu sha’awar tsayawa takarar kujeru mabanbanta ba su fito suka fara nuna sha’awar tsayawa ba duk sauran yan kwanaki ƙalilan an gudanar da zaben? Wadannan su ne tambayoyin masu sharhi a kan harkokin siyasa da ma wasu daga cikin ‘yan siyasa jihar Katsina.

Ga wasu mutum biyar, waɗanda ake kyautata zaton ɗaya daga cikin su zai samu zarafin ɗarewa kujerar shugabancin jam’iyyar APC a Jihar Katsina:

MALAM SHITU SHU’AIBU SHITU: Shi ne Shugaban Kwamitin Riko na jam’iyyar APC a Jihar Katsina a halin yanzu. Malam Shitu gogaggen dan siyasa, wanda tun da aka dawo mulkin damakaradiyya a shekarar 1999, bai taba sauya sheka ko ya bi wata jami’yya mai mulki ba, jam’iyyar adawa aka san shi ta shugaban kasa muhammadu Buhari har aka kai ga yin nasara a shekarar 2015.

Malam Shitu S. Shitu a zaben shugabannin jam’iyyar APC ta gudanar bayan dunkulewar jam’iyyu wato Maja a shekarar 2014, ya zama jami’in hulda da jama’a da yan jaridu na jamiyyar APC na jihar Katsina a lokacin da aka zabi Malam Mustapha Muhammad Inuwa a matsayin shugabantan na jiha. Bayan samun nasarar zabe da jam’iyyar APC ta samu a jihar Katsina, sai gwamna Aminu Bello Masari ya nada Malam Mustapha Inuwa, sakataren gwamnatin jihar Katsina, inda aka samu gurbi na shugabancin jam’iyyar a lokacin. Sai aka dauko mukkadashin shugaban jam’iyyar na jiha, Abdulkadir Mamman Nasir da ya fito daga shiyya daya da gwamna Masari daga baya aka ba shi Mamman Nasir mukamin mai baiwa gwamna shawara.

Tafiyar Abdulkadir Mamman Nasir ke da wuya aka baiwa jami’in hulda da jama’a da kuma ‘yan jaridu watau (State Public Relation Officer) rikon tafiyar da shugabancin jamiyyar har zuwa a lokacin da aka gudanar da zaben shugabannin jam’iyyar, inda malam Shitu ya zama shugaban jam’iyyar APC mai cikakken iko kuma zababbe.

Malam Shitu S. Shitu kusan shi ne shugaban jam’iyyar APC mafi dade wa kuma shugaban da jam’iyyarsa ke mulkin jihar Katsina da kasar karkashin shugabanci muhammadu Buhari, wanda shima dan asalin jihar Katsina. Haka zalika shugaban rikon na jam’iyyar , an tabbatar yana samu goyan bayan sakataren gwamnatin jihar Katsina, wanda kuma shi ne shugabanta na farko a jihar Katsina.

Malam Shitu yana daya daga cikin wadanda ake ganin zai iya samun nasarar kara darewa bisa wannan kujera ganin cewa dai farko shi ke rike da ita jam’iyyar APC a halin yanzu, na biyu masu sharhi na ganin zai wuyar gaske gwamna Aminu Bello Masari ya juya masa baya ganin irin yadda aka taho a siyasance tare. Na ukku duk wadanda ake hasashen za su yi takarar kusan ya fi su karfin tattalin arzki ko da ace ba zai samu goyan baya daga wasu bangarorin.

Kalubalen da masu sharhi ke ganin zai iya fuskanta na kara darewa kan wannan kujerar, shi ne idan jam’iyyar ta ce za ta duba yiwu war karba-karbar shugabancin a shiyyar Daura da Funtua ko kuma dan takarar gwamna daga wace shiyyar zai fito? Na biyu akwai kalubalen sauran ‘yan takarar gwamnan 2023 da wasu jiga-jigan jam’iyyar da suke ganin ya dauki bangaren takarar Mustapha Inuwa, Sakataren gwamnatin jihar Katsina, wanda ake sa ran zai tsaya takara kuma ga shi amininsa ne, masu sharhi da dama suna ganin wadanan jiga-jigan musamman masu rike da mukaman siyasa a Abuja kuma don son sha’awar tsayawa takara a 2023, za su hada-kai su yaki takarar ta shi.

BALA ABU MUSAWA: Yanzu haka shi ne Mataimakin Shugaban jam’iyyar na shiyyar dan majalisar dattawa na Funtua. Kuma daya daga cikin na hannun-damar gogaggen dan siyasar nan na Najeriya da jihar Katsina, Sanata Abu Ibrahim, wanda an yi ittifakin yaransa ne suka mamaye kafatanin shugabanci jam’iyyar a kowane mataki a yankin Funtua. Ana ganin idan Sanata Abu Ibrahim ya tsayar da Alhaji Bala Abu Musawa, akwai yiwuwar ya samu nasara.

Bala Abu Musawa kuma (Cigarin Musawa)dan siyasa ne da ya ga jiya ya kuma ga yau, kwararre ne wajen iya kalaman jan hankali siyasa, wadanda magoya baya na jin dadin kalaman sa, kusan a halin yanzu yana daga cikin wadanda ake ganin gogewar sa ganin ba shi da tsoro. Amma har zuwa hada wannan rohatan babu wata majiya da ta tabbatar da cewa ya nuna zai tsaya takarar shugabancin jam’iyyar APC a jihar Katsina. Masu sharhi na cewa sau da yawa wajen tarurruka, magoya bayansa na cewa “sai ka yi shugaban jam’iyyar a jihar Katsina’’ an ga yana fara’a da dariya duk lokacin da aka yi masa wannan fatan. Wasu na ganin kamar yana samu goyan bayan mafi rinjayen yan majalisar jiha kuma suna yawan ganawar sirri ta yadda za’a hudo ma samun nasarar cin zaben shugabanci jam’iiyyar. Hatta Matasan yan siyasa suna kallonsa a matsayin wani jigo ko bango sukari duk wanda ya rabe shi sai ya lasa. Farin jinin Bala Abu Musawa ya karade kowacce shiyya, kusan duk cikin mataimakan shugaban jam’iyyar na sauran shiyyar babu mai farin jinin sa a halin yanzu, an yi ittifakin abin hannun shi bai rufe mashi Ido ba ko miskala zarratan, kullum kokarinsa ya samu ya bayar. Mutane na ji dadin faran-faran dinsa da jama’a, da wuya ka ga bacin ransa, yana da kunnuwan sauraren al’umma, ba tare da gajiyawa ba.

Kalubalen da zai iya fuskanta shi ne ubangidan sa, Sanata Abu Ibrahim ya sauka daga sanatan kuma ba shi cikin gwamnati a matakin jiha da na tarayya, amma yana da tsohuwar alaka da jigo a jam’iyyar APC na kasa kuma tsohan gwamnan jihar Legas, Alhaji Bola Ahmad Tinubu. Idan kuma idan har jam’iyyar APC ta tsaida dan takara daga shiyyar Funtua, nan ma zai iya zame ma takarar ta samu tasgaro. Haka zalika, ana ganin sa wajen tarukan Ahmad Dangiwa, Shugaban Banki Bada Lamunin Gidaje Na Kasa da tarukan Shugaban Hukumar Kula Da Kananan Da Matsakaitan Sana’o’I ta kasa Dr. Dikko Radda, ana ganin kamar suna sunsunar tsayawa takarar gwamnan jihar Katsina. Lokaci dai ne kadai zai bayyana sauran dalilan da kalubalen.

SALLAU ARAWA: Dan siyasa ne da ya fito daga kudancin Katsina daga karamar hukumar Dandume a jihar Katsina. Ya taba neman tsayawa takarar mataimakin shugaban jamiyyar na shiyyar Funtua wand abai samu nasara ba, Bala Abu Musawa. Alhaji Sallau Arawa shi ne na hannun damar shugabar Hukumar Kula Da Tashohin Jiragen Ruwa Ta Kasa, Hajia Hadiza Bala Usman. Idan ta goyin bayansa dari bisa dari yay i tasiri sosai a zabe mai zuwa na shugabannin jam’iyyar da yake tafe. Yanzu haka yana shugabantar wata kungiya ta tuntuba dake kananan hukumomi goma sha daya na yanki Funtua, mai rajin kare da zaman jam’iyyar APC day aba tare da tabbatar da hadin kan jam’iyyar APC a shiyyar.

Yanzu babban kalubalen da zai kara fuskanta shi ne yadda fadar shugaban kasa ta dakatar da uwar dakinsa daga shugabanci Hukuma kula da tashoshin jiragen ruwa kuma an kafa kwamitin bincikarta. Zai wahalar gaske har a wanke ta kafin zaben shugabanni jam’iyyar da ake sa ran yi nan gaba kadan. Ana iya cewa yanzu da shi da ita idan ana ta kai ba’a ta kaya.

SABO MUSA: Shi ne shugaban shahararriyar kungiyar nan ta Masari Restoration Awareness Forum kuma babban mai taimaka wa gwamna Masari Kan Dawo Da Martabar Jihar Katsina. Alhaji Sabo ya kwashe sama da shekara arba’in yana gudanar da harkokin siyasa a matakai daban daban. Yana da kyakkyawar alaka da manyan jiga-jigan jam’iyyar APC a jihar Katsina kamar su mai girma gwamna Alhaji Aminu Bello Masari da mataimakinsa Alhaji Mannir Yakubu da kuma jigo a jam’iyyar a jihar Katsina, Alhaji Dahiru Barau Mangal da kuma kungiyoyin matasa. Sabo Musa yana rike da sarautun gargajiya guda biyu Majidadin Magajin Gari da Malumman Bakori. Kalubalen da zai iya fuskanta akwai yanayin dangantakarsa da masu ruwa da tsaki a matakai daban daban. Amma yana da kyakkyawar alaka da jam’ian gwamnati da kuma masu karamin karfi. Ko da yaushe kofar sa a bude take wajen sauraren korafe korafe alumma domin mikawa gwamnati. An shedi shi da taimakon alumma, musamman ga wadanda bas u samun kaiwa ga gwamnati yana zame masu tsani.

SANATA ABBA ALI: Yanzu haka shi ne mataimakin shugaban riko na kasa jam’iyyar APC mai kula da shiyyar Arewa Maso Yamma dake kula da jihohin Kano da Kaduna da Jigawa da Katsina da Sokoto da Kebbi da kuma Zamfara.

Dattijo sanata Abba Ali abokin makarantar shugaban kasa Muhammadu Buhari ne kuma na daya daga cikin na hannun damarsa. Masu sharhi na ganin kamar wannnan damar shugabancin riko na wannan shiyya ta arewa maso yamma wata dam ace ta ya zama zababbaen shugaban jam’iyyar na jihar Katsina.

Alhaji Abba Ali, kwararren dan siyasa ne da aka dade ana damawa da shi, yay i sanata tun lokacin shugaban kasa marigayi Alhaji Shehu Shagari. Duk bait aba furta cewa yana son tsayawa shugabancin jam’iyyar a jihar Katsina ba, amma da dama mutane na has ashen kamar yana son kujerar. Wasu kuma na alakanta shi da takarar gwamna da sanata Hadi Sirika ake kyautata zaton zai iya yi a shekarar 2023 idan Allah ya kaimu.

Kalubalen da zai iya fuskanta akwai yawan shekaru da yake da su, kuma dangatakar da shugabanni da wakilan jam’iyyar APC a matakai daban daban, saboda akwai tazararsa tsakaninsa da al’umma ko masu zabe. Bai rike wani mukamin a kwanakin nan ko dawo war siyasa kuma ba mukamin da ya rike a jihar Katsina.

MALAM KABIR MURJA: Gogaggen dan siyasa ne, wanda shima tsohan dan adawa, bait aba shiga jam’iyyar PDP ba, ana kiransa farfesan siyasa a jihar Katsina. Ya taba tsayawa takarar shugabancin jam’iyyar APC a shekarar 2014, a lokacin yana samun goyan bayan Sanata Injiniya Mahmud Kanti Bello. Haka kuma ya so tsayawa a lokacin da aka tsaida Malam Shitu takarar shugabanci APC, yayin da ya jagoranci tsagen APC Akida, wanda ake kyautata tsammani dan shahararren dan kasuwar nan kuma aminin shugaban kasa, sirikin shugaban kasa Buhari, Abubakar Sama’ila Isah yak e daukar nauyinsa.

Kalubalen da zai fuskanta a wannan karon shi ne wadannan iyayen gida nasa watau Sanata Mahmud Kanti Bello da mahaifin Abubakar Sama’ila duk sun rasu a lokaci mabanbanta. Dole ya sake lissafi, duk da masanin siyasar cin zabe ne, saboda harkar zabe na bukatar masu gida rana ko kuma wanda zai dauki nauyin kashe ma kudin. Wata majiyar ma ta ce jam’iyyar ba ta sabunta katin zamansa dan jam’iyya da ake cikin yi a halin, idan kau har babu katin zama dan jam’iyya babu yadda za’a yi ya tsaya takara shugabancin jam’iyya na kowane mataki , shi yasa ake masu sharhi ke ganin kamar yana da wuyar gaske ya samu nasarar.

Kujerar Shugabancin jam’iyyar APC muna iya cewa za ta iya zama allura cikin ruwa. Saboda na farko dai idan aka ce za’a bi tsarin karba-karba tsakanin shiyyoyin Katsina da Daura da kuma Funtua, nan ma za’a iya zaftare wasu masu Sha’awar tsayawa takarar, akwai yiwuwar kuma ace su masu rike da shugabanci karkashin Malam Shitu da mataimakansa Alhaji Bala Abu Musawa da Mamman Yaro Batsari da kuma Alhaji Usman Osi da zauran shugabanni su ci gaba da tafiyar ragamar jam’iyyar.

Yanzu dai babban abun jira a gani uwar jam’iyyar ta Kasa ta Fito da sharudda da Tsare tsaren yadda za’a gudanar da zaben, wanda har zuwa hada wannan rohatan babu jaddawalin zaben. Kuma akwai yiwuwar nan gaba wasu su kara fitowa ko nuna Sha’awar tsayawa. Saboda su ma wadannan mutane bakwai har yanzu babu wanda ya fito fili ya fara yakin neman a zabe shi kan wannan kujera. Abinda ake jira yanzu a sanya rana da Tsare-tsaren zaben. Lokaci kadai zai tabbatar da wanda ke da rabonta.