“Allah zai ƙara baiwa Najeriya shugaba mai kishi irin Buhari” Gwwmnan Ebonyi

Raba a Facebook

Tura zuwa Twitter

Gwamnan jihar Ebonyi Dave Umahi ya yi addu’ar Allah ya sake ba wa ƴan ƙasar shugaba mai kyakkyawar zuciya da kishin kasa kamar shugaba Muhammadu Buhari a zaɓen 2023.

Ya bayyana haka ne a zantawarsa da manema labarai jim kaɗan bayan ganawa da shugaba Buhari a fadar shugaban ƙasa a Abuja, inda yace ya je ne domin miƙa masa godiya ta musamman saboda yadda yake ɗaukar yankin da muhimmanci.
Gov. Umahi tare da Buhari jiya Litinin a fadar shugaban ƙasa.
Jaridar Punch ta rawaito gwamnan na jinjina wa shugaban ƙasa kan wasu manyan ayyukan ci gaba da gwamnatinsa ta samar a yankin kudu maso gabas ciki har da aikin gadan Second Niger da yanzu ya kama hanyar kammaluwa da kuma aikin layin dogo wanda a cewar sa zai bunƙasa harkokin kasuwanci a yankin.

Share this:

Raarraba

Facebook

Twitter

Labarin bayaBayan Zamfara, Sojoji sun kashe ƴan-fashin daji sama da 50 a Kaduna

Hausa Daily Times ingantacciyar kafar yaɗa labarai ce dake da ƙwararrun ma’akata ƙarƙashin jagorancin ƙwararrun ƴan jaridu.