AFCON: Kasar Afirka Ta Kudu Ta Mayar Wa Ofishin Jakadancin Najeriya Martani Akan Kalamunta

Ofishin Hulda da Kasashen Waje na Afirka ta Kudu  (DIRCO) ya mayar wa Ofishin Jakadancin Najeriya martani kan wata sanarwa da ta fitar tana bawa ‘yan Najeriya mazauna Afirka ta Kudu shawarar gudanar da bikin murna idan harSuper Eagle tayi nasara akan Bafana-Bafana.