Liverpool ta sake yin wani gwaninta wajen kai hari inda ta lallasa Southampton da ci 4-0 wanda hakan ya sa kungiyar ta tsallake zuwa mataki na daya a teburin gasar Premier ta Ingila. Kungiyar ta Reds sun ci akalla kwallaye biyu a wasanni 17 da suka yi a duk gasa.