Yau Rana Ta Biyar A Olympic: Ghana Ta Kuma Sake Nasara A Damben Boxing

Dan damben boxing Ghana Samuel Takyi ya lallasa Jean Carlos Caicedo dan kasar Ecuador ta hanyar hukuncin bai daya da alkalai suka yanke, lamarin da ya bashi damar ketarawa zuwa matsayi na gaba a gasar Olympic a birnin Tokyo.