AFCON 2023: Yan Wasan Najeriya Sun Isa Abuja

‘Yan wasa 10 na kungiyar kwallon kafar Najeriya ta Super Eagles da ke taka leda a kasashen Turai sun isa Abuja babban birin kasar, gabanin fafata wasanni biyu na neman gurbin gasar cin kofin nahiyar Afirka da kasar za ta buga da Guinea Bissau.