Umar Bago na APC ya lashe zaben gwamnan Neja

Dan takarar jami’yyar APC Umar Bago ya lashe zaben gwamnan jihar Neja.
Baturen zabe Kuma Shugaban Jami’ar Abuja, Clement Alawa ya sanar da sakamakon zaben a garin Minna ranar Litini.
Alawa ya ce Bago ya samu kuri’u 469,896 da ya kada abokin takarar sa Isah Liman-Kantigi na jami’yyar PDP da ya samu kuri’u 387,476.
Ya ce Joshua Bawa na jami’yyar LP ya samu kuri’u 3,415 sai kuma Ibrahim Yahaya daga jami’yyar NNPP da ya samu kuri’u 3,378.
Alawa ya ce jami’yyar ADP ta samu kuri’u 2001, jami’yyar APGA ya samu kuri’u 1,746 sannan jami’yyar PRP ya samu kuri’u 992.
Jami’yyar NRM ya samu kuri’u 969, jami’yyar SDP’ kuri’u 908, Jami’yyar ADC ta samu kuri’u 665, AA ta samu kuri’u 471, YPP ya samu kuri’u 445, APM ya samu kuri’u 351, APP 167, Accord ta samu kuri’u 140.
Ya ce mutum 2,698,344 ne suka yi rajista a jihar amma mutum 899,488 suka kada kuri’a zaben jihar.
An kada kuri’u 889,950 inda daga ciki an samu kuri’u 873,020 masu kyau, 26,936 lalatattu.
Zaben ya gudana a rumfunar zabe 4,950 a kananan hukumomi 25 a jihar.