A jihar Diffa ta Jamhuriyyar Nijar, manoman shinkafa fiye da duba-daya suka yi asarar shinkafar da suka noma a bana sakamakon bayyanar wasu tsuntsaye masu tarin yawa wadanda suka fito daga kasar Chadi mai makwbtaka da jihar. A cewar manoman, a tarihi ba su taba ganin irin wannan al’amarin ba.