2023: Osinbajo ya fi dacewa ya gaji Buhari – Ɗan majalisan Kano, Kawu

Ɗan majalisan dake wakiltar Tarauni a majalisar Wakilai ta Tarayya, Hafiz Kawu ya bayyana cewa mataimakin shugaban Kasa Yemi Osinbajo ne ya fi cancanta ya gaji Shugaban Kasa Muhammadu Buhari.

” Na yi aiki da mataimakin shugaban ƙasa Yemi Osinbajo na tsawon shekara. Mutum ne mai dattaku da sanin ya kamata wanda zai iya kawo karshen matsaloli da kai Najeriya ga ci.

Kawu ya ce duk da yana yin wannan abu ba da sani ko umarnin Osinbajo bane a nashi ganin mataimakin shugaban kasan ya cancanta a bashi dama bayan shugaba Buhari ya kammala mulkin sa.

” Osinbajo kwararre ne sannan masani ga shi kuma ya na da natsuwa ta addini. Lallai ya cancanci a bashi dama a 2023 domin ya kwarara sanin sa da basirarsa don ci gaban kasar nan.