2023: OPC ba ta cikin gamayyar ƙungiyoyin da ke wa Tinubu ko wani ɗan kudu jagaliyancin neman shugaban ƙasa

Ƙungiyar Kare Muradun Yarabawa Zalla (OPC), ta nesanta kan ta daga gungun wasu ƙungiyoyin Yarabawa 57 masu yunƙurin ganin an tsayar da Bayarabe takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023.

Cikin wata sanarwa da Kakakin Yaɗa Labarai na OPC, Yinka Oguntimehin ya fitar a ranar Litinin, ya nesanta OPC da shugaban ta Gani Adams daga ƙungiyoyin da aka ce na so ko dai Bola Tinubu, Yemi Osinbajo ko Kayode Fayemi ɗaya ya tsaya kuma ya ci zaɓen 2023 na shugaban ƙasa.

OPC ta ce haɗa sunan ta da sauran ƙungiyoyin da ke goyon bayan wannan yunƙurin zamba ce kuma ƙarya ce kawai domin neman wani suna ko cimma biyan wata buƙata kawai.

Kungiyoyin dai sun yi taro a ranar Asabar a Lagos, inda su ka yi matsaya cewa ko dai Tinubu ya fito takara, ko Mataimakin Shugaban Ƙasa Yemi Osinbajo ya fito, ko kuma Gwamna Kayode Fayemi na Ekiti ya fito.

Sun yi taron ne a ƙarƙashin jagorancin wani fitaccen ɗan jarida Adewale Adeoye, inda bayan tashi daga taron, Femi Agbana da Ganiat Toriola su ka sa wa takardar bayan taro hannu.

Tuni dai wasu su ka fara yi wa Tinubu kamfen, inda a Kano gungun wasu malamai su 2500 suka yi wa Tinubu addu’ar neman nasara.