2023: Ba na goyon bayan kowane ɗan takara, inji Jonathan a gaban Tinubu

Kwanaki uku bayan tsohon Shugaban Ƙasa Olusegun Obasanjo ya bayyana cewa ba ya goyon bayan kowane ɗan i shugaban ƙasa a zaɓen 2023, shi ma takwaran sa Goodluck Jonathan ya ce kowa ta sa ta fis she shi, ba zai goyi bayan kowane ɗan takara ba.
Jonathan ya bayyana haka a Abuja wurin taron taya Babban Limamin Kirista, Mathew Hassan-Kukah murnai cika shekaru 70 da haihuwa.
A wurin taron an kuma ƙaddamar da gidauniyar gina Cibiyar Nazarin Nagartacciyar Gwamnati ta Hassan Kukah.
Jonathan ya bayyana matsayar sa kwanaki biyu bayan ɗan takarar shugaban ƙasa na APC, Bola Tinubu ya kai masa ziyara a gidan sa na Abuja.
A wurin taron Hassan Kukah, Tinubu da mataimakin takarar sa duk sun halarta, kuma a gaban su Jonathan ya ce babu ruwan sa da kowane ɗan takara.
Jonathan ya kuma ja hankalin masu mulki cewa su riƙa juriya da masu adawa, domin dimokraɗiyya ba wai cin zaɓe kaɗai ba ce, adawa na cikin dimokraɗiyya. Inji Jonathan.
Ya kuma yi ƙorafin yadda musamman gwamnoni ke mulkin kama-karya a jihohin su.
PREMIUM TIMES Hausa ta buga cewa Obasanjo ya ce, ‘ba na goyon bayan kowane ɗan takara a 2023, kowa ta sa ta fisshe shi kawai.’
Tsohon Shugaban Ƙasa Olusegun Obasanjo ya bayyana cewa a zaɓen 2023 ba ya goyon bayan kowane ɗan takara.
Da ya ke magana da manema labarai bayan ya fito daga ziyarar da ya kai gidan tsohon Shugaban Mulkin Soja, Janar Abdulsalam Abubakar, Obasanjo ya ce daga nan har a yi zaɓe ba ya goyon bayan kowane ɗan takara.
Ya bayyana haka makonni biyu kenan bayan ɗan takarar shugaban ƙasa na APC Bola Tinubu ya kai masa ziyarar, inda daga baya Obasanjo ɗin shi ma ya ce bai ce ya na goyon bayan sa ba, kuma bai ce ba ya goyon bayan sa ba.
Sannan kuma idan ba a manta ba cikin makon jiya Obasanjo ya yi ganawa da fanɗararren jigon PDP a Landan, wato Gwamna Nyesom Wike na Jihar Ribas.
A Minna, Obasanjo ya ce ba batun siyasa ya kai shi ba, ya ce duniyar Janar Abubakar ne saboda jinyar da ya sha a asibitin Landan.
“Na zo duba ɗan uwa na ne, saboda ya yi fama da rashin lafiya. Da na tafi Landan na yi niyyar zuba na duba shi, amma sai mu ka yi saɓani, ranar na na isa, shi kuma a ranar ya dawo Najeriya.
“Dalili kenan na ce bari na zo har Minna na duba shi, tunda ni ma na dawo gida.
“Duk wani makusanci na in dai ba ya jin daɗin jikin sa, zan je na duba shi, tunda ni dai lafiya ta garau har yanzu ina jin jiki na da ƙwari.” Inji Obasanjo.
Bayan ziyarar da ya kai gidan Abubakar, Obasanjo ya zarce sun gana da tsohon Shugaban Ƙasa Ibrahim Babangida.
A zaɓen 2011 dai Obasanjo ya goyi bayan Goodluck Jonathan. Sai dai kuma a 2015 ya goyi bayan Muhammadu Buhari na APC bayan ya kekketa katin sa na mamba ɗin PDP.
A zaɓen 2019 kuma Obasanjo ya goyi bayan Atiku Abubakar na PDP.