Ɗan gidogar kwangila ya yi barazanar kashe wakilin PREMIUM TIMES, saboda ya fallasa amaja a gine-ginen da ya yi wa gwamnati

Wani ɗan kwangilar da ya yi aikin kula da gine-gine a Jihar Akwa Ibom, ya yi barazanar kashe wakilin PREMIUM TIMES, saboda ya fallasa yadda aka yi ha’inci wurin aikin gine-ginen.
Kwanan baya PREMIUM TIMES ta buga labarin yadda aka yi amaja da ha’inci wajen aikin gina rumfunan kasuwa guda 30 a Abiakpo, al’ummar da ke zaune a Ƙaramar Hukumar Obot Akara, Jihar Akwa Ibom.
An buga labarin yadda gine-ginen su ka lalace watanni takwas kacal bayan gina su, ginin da aka tabbatar cewa an yi amfani da kayan gini masara inganci da nagarta.
Sanata Christopher Ekpenyong, mai wakiltar Akwa Ibom Shiyyar Arewa maso Yamma ne ya kai aikin ginin a garin, kuma an yi ginin kusa da gidan sa.
Wasu kantinan bangon su ya tsage, wasu bangayen kuma duk sun yi rami, sun huje a rufin su. Haka nan kuma daɓen simintin wasu kantinan duk ya gurgure.
Sannan kuma idan iska ya dan filfila ko ba da ƙarfi ba, yawancin rufin kwanon ya na fafarniya da faffaka, kamar iska zai kwaye su.
Sannan kuma wakilin mu ya ruwaito cewa ba a kafa ko gina isassun dirkoki ba. Haka nan kuma a wasu kantinan maimakon a yi dirkoki ginin bulo-da-bulo, sai aka tokare rufin da itacen gora. Hakan kuwa ya haifar da damuwa a zukatan mazauna yankin, saboda tsoron a ko da yaushe gini zai iya rufto masu.
Cibiyar Binciken Ayyukan Gini da Tirina ta NBRRI ce ta bai wa kamfanin Tymme Energy Integrated Resources Limited aikin ginin.
Kamfanin dai a garin Kabba a Jihar Kogi ya ke, kuma an yi masa rajista a cikin 2018, ranar 16 Ga Fabrairu.
Mazauna garin da su ka yi hira da wakilin mu, sun yi kira ga ɗan kwangilar ya sake aikin baki ɗaya.
Yayin da wakilin PREMIUM TIMES Saviour Imukudo ya tuntuɓi babban jami’in kwangilar mai suna Andrew Okure, wanda ya yi aikin gyaran rumfunan, sai ya ƙi yin magana.
Sai dai kuma bayan ya karanta labarin a ranar Laraba, ya kira wakilin mu ya riƙa yi masa bambami.
Ya ce wai waɗanda su ka yi ƙorafi kan aikin “duk ‘yan jam’iyyyar adawa ne.”
Sai dai kuma washegari wakilin mu ya nemi jin ta bakin sa a ranar Alhamis, sai ya ce masa, “zan bi ka sai na cim maka. Ka bi a hankali, ka bi a hankali.”
A gefen sa kuma wakilin mu ya ji wata murya na cewa, “ai mun gane ka, mun san sunan ka, wani can na yi masa turin-je-ka-ka-mutu, kai kuma ka na biye ma ko.”
Babban wakilin PREMIUM TIMES na Shiyyar Kudu maso Kudu, Cletus Ukpong, ya bayyana cewa babu wanda ya isa ya yi wa PREMIUM TIMES ko wakilan ta wata barazanar da za a ji tsoron fallasa duk wata almundahana da ya yi.