Ɗan cikas ɗin da aka samu a zaɓen shugaban ƙasa bai isa ya sauya sakamakon zaɓe ba – Matsayar rundunar Tinubu

Rundunar Yaƙin Neman Zaɓen Bola Tinubu ta fantsama taron ganawa da manyan ‘yan jaridu na duniya, a ƙoƙarin da ta ke yi na kare halasci da cancantar nasarar lashe zaɓen da Tinubu ya yi a ƙarƙashin jam’iyyar APC.
Tawagar wadda ke ƙarƙashin Ƙaramin Ministan Ƙwadago, Festus Keyamo, ta gana da ‘yan jarida a Cibiyar ‘Yan Jarida ta Amurka da ke birnin Washington D.C a ranar Laraba.
Keyamo wanda ya kasance shi ne Kakakin Yaƙin Neman Zaɓe, ta shaida wa manema labarai cewa cikas da ‘yan matsalolin da aka fuskanta a lokacin zaɓen shugaban ƙasa ba 2023 har ma da rikici, sun faru ne a ƙasa da kashi ɗaya bisa 100 ilahirin yawan rumfunan zaɓe da ke faɗin Najeriya.
“Saboda haka ba su kai yawan da za a ce ai za su iya canja sakamakon zaɓen ba.”
“Rahotannin faruwar faɗace-faɗace da cikas a wasu rumfunan zaɓe ba za su isa su sauya alƙaluman zaɓe ba. Akwai rumfunan zaɓe 176,974 a Najeriya. Inda aka samu hatsaniya da cikas ɓa su kai ko kashi 1 bisa 100 na yawan rumfunan zaɓen ƙasar ba .”
Dama kuma a baya-bayan nan sai da Ministan Yaɗa Labarai Lai Mohammed ya ziyaraci Amurka da Birtaniya bayan kammala zaɓe.
Zaɓen Shugaban Ƙasa: Buhari Da Gwamnoni 20 Ba Su Kawo Jihohin Su Ba – Keyamo
Yayin da Festus Keyamo ke ƙoƙarin nuna wa ‘yan jaridar Amurka sahihancin zaɓen 2023, ya nuna masu cewa Shugaba Muhammadu Buhari da wasu jiga-jigan APC masu yawa ciki har da gwamnoni 20 duk ba su yi nasarar zuwa na ɗaya a yawan ƙuri’un jihohin su ba.
“A karo na farko gwamnoni 20 da ke kan mulki duk ba su kawo yawan ƙuri’un da aka jefa a jihohin su ba. Kuma gwamnoni bakwai da su ka nemi sanata duk an kayar da su. Wannan kuma ba ta taɓa faruwa kamar haka a tarihin zaɓen Najeriya ba.
“Shi ma zaɓaɓɓen shugaban ƙasa Bola Tinubu an kayar da shi a Jihar Legas, jihar sa ta haihuwa. Shugaba Buhari bai kawo jihar Katsina ba. Daraktan Kamfen na APC, Simon Lalong bai kawo jihar Filato ba. Shi ma Shugaban APC, Abdullahi Adamu shi ma bai kawo jihar Nassarawa ba. Haka Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin APC, Atiku Bagudu bai yi nasara a Kebbi a zaɓen shugaban ƙasa ba, kuma an kayar da shi.
Keyamo ya ce mutum 23 ne su ka mutum yayin zaɓen 2023. Amma ya ce a zaɓen 2019 an kashe mutum 150.
“Zaɓen 2011 an kashe mutum 800, na 2015 an kashe mutum 100. Na 2019 an kashe mutum 150. Amma na 2023 mutum 28 aka kashe. Kenan masu cewa zaɓen 2023 ya fi sauran zaɓuka muni, hakan ba gaskiya ba ce.”