Ƴan bindiga na tsare da ɗaliban Islamiyyar Tegina cikin mummunan yanayi – Cewar ɗan aiken kai ƙuɗin fansa

An sako mutumin nan da ‘yan bindiga su ka tsare, bisa zargin kuɗin somin-taɓin biyan fansar ɗaliban Tegina 137 ba su cika ba, sai dai kuma ya bayyana irin halin ƙuncin da yaran ke ciki a hannun ‘yan bindigar.

An sace yaran da ƙarfin tsiya lokacin da su ke tsakiyar karatu a Salihu Tanko Islamiyya School, a Tegina, Jihar Neja tun a ranar 30 Ga Mayu.

Ya bayyana halin da yaran ke ciki, waɗanda yawancin su kwanyamin yara ne ƙanana, bayan an sake shi a ranar Litinin.

PREMIUM TIMES ta buga labarin yadda aka tura Ƙasimu Barangana da wasu mutane shida domin kai kuɗin fansa. Sai dai kuma sun riƙe Barangana bayan da su ka ƙirga kuɗi su ga ce ba su cika ba.

Barangana ya shaida wa PREMIUM TIMES Hausa bayan ya kuɓuta cewa sun raba yaran a matsugunai daban-daban, inda su ka kasa su a sansanoni 25.

“An karkasa su wurare 25 a cikin dajin. Kowane kashi wasu ‘yan bindiga ke tsare da su, saboda tsoron kai masu hari.

“Sun kai ni sun zagaya da ni, duk na ga halin da su ke ciki. Gaskiya su na cikin wani mawuyacin hali abin tausayi.” Inji Barangana.

Ya ce ‘yan bindiga ba su doke shi ko wulaƙanta shi ba.

Na Riƙa Cin Naman Shanu Ina Ƙoshi, Kuma Su Ka Damƙa Min Kuɗin Mota Naira 11,000 -Barangana

“Lokacin da su ka tsare ni a cikin jeji sun kula da ni. Har na baro dajin naman shanu su ke ba ni ina ci ina ƙoashi. Da su ka sallame ni kuma, su ka ba ni kuɗin mota naira 11,000.

“Amma fa a gaskiya ban san ranar da za su saki yaran nan ba, domin yanzu haka su na jiran sai mun ƙara kai masu sabbin babura guda biyar sannan su sake su.” Inji shi.

Wani malamin makarantar mai suna Yakubu Idris ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa sun kai naira miliyan 25, su ka ƙara kai wa ‘yan bindigar naira miliyan 30 kuma. Shugaban makarantar ya shaida wa wakilin su cewa yawancin iyayen yaran sun sayar da gonakin su ne, kuma aka tsagi sashen makarantar aka sayar don a haɗa kuɗaɗen da aka kai wa ‘yan bindigar.