ZAZZABIN CIZON SAURO: WHO ta yi kira ga kasashen Afrika su ware isassun kudade domin dakile yaduwar cutar

Kungiyar kiwon lafiya ta duniya WHO ta yi kira ga shugabanin kasashen Afrika da su ware isassun kudade domin dakile yaduwar Zazzabin cizon sauro a yankin.

Wakilin WHO a Najeriya Walter Mulombo ne ya yi wannan kira a Wani zama da aka yi domin Shirin taron ranar zazzabin cizon sauro ta duniya na shekarar 2023 da aka yi a Abuja ranar Talata.

Mulombo ya ce hakkin gwamnati ne ta Samar da kudaden da ake bukata domin dakile yaduwar cutar ta hanyar inganta cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko domin tallafa wa mutanen da su ka fi bukatan maganin.

Ya ce yin haka zai taimaka wajen inganta samar da magunguna da karfafa hanyoyin dakile yaduwar cutar a Afrika.

Mulombo ya ce Afrika ta yi kokari wajen inganta fannin lafiyar ta ssi dai har yanzu akwai aikin da ya kamata a yi domin dakile yaduwar cutar.

Ya ce duk da cewa kokarin da ake yi na ganin an dakile yaduwar cutar har yanzu cutar na ci gaba da kisan mutane da dama a Afrika tun a shekarar 2015.

Yaduwar Zazzabin cizon sauro

A shekarar 2020 akalla mutum miliyan 241 ne suka kamu da cutar yayin da cutar ta kashe mutum 627,000 a kasashe 85.