ZANGA-ZANGAR NLC A KADUNA: NUPENG ta yi barazanar dakatar da raba mai da iskar Gas a Najeriya

Kungiyar ma’aikatan man fetur da iskar gas ta kasa ta gargadi gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai, ya shiga taitayin sa kan yadda ake kaiwa masu zanga-zangar Kungiyar Kwadago hari a Kaduna.

Kungiyar NUPENG ta ce idan wasu suka sake tsangama NLC a wajen zanga-zanga, zamu dakatar da jigilar mai da iskar gas a fadin Kasar nan karkaf.

” Wannan gargadi ne mai mahimmanci, a tabbata an bishi sau da kafa ko kuma duk kasa a kwan ciki.”