Zanga-zanga Old Trafford Ta Sa An Dage Wasan United Da Liverpool

Boren ya samo asali ne bayan da magoya bayan United suka fito don nuna adawarsu ga iyalan Glazers da suka mallaki kungiyar ta Manchester United, saboda sun goyi bayan kirkirar sabuwar gasar Super League da aka fasa.