ZAMFARA: ‘Yan bindiga sun kashe mutum 8 da suka yi garkuwa da su saboda ‘yan uwansu basu biya kudin fansa ba

‘Yan bindiga kuma yaran shahararren dan bindiga Dankarami sun kashe mutum 8 daga cikin mutum 10 din da suka yi garkuwa da su daga karamar hukumar Zurmi a jihar Zamfara.

‘Yan bindigan sun kashe wadannan mutane saboda ‘yan uwansu sun ƙasa biyan kudin fansan naira miliyan 6.

‘Yan bindigan sun yi garkuwa da wadannan mutane ranar 1 ga Satumbar 2021 bayan sun yi kokarin kai wa hedikwatar karamar hukumar Zurmi hari.

Ganin sun ƙasa kai wa hedikwatar karamar hukumar hari sai washe gari ‘yan bindigan suka sace mutum 10 daga karamar hukumar.

A cikin farkon makonni shekarar 2022 an kashe mutum 486 inda mafi yawan su ‘yan bindiga ne suka kashe su.

Mutum biyu daga cikin mutum 10 da aka yi garkuwa da su sun gudu.

Wani shugaban kungiyar matasa dake karamar hukumar Zurmi, Abdullahi Muhammad, ya bayyan wa PREMIUM TIMES cewa bayan makonni biyu da yin garkuwa da mutanen mutum biyu sun gudu.

“Ina cikin mutanen da suka karbi mutum biyu din da suka arce daga hannun ‘yan bindigan.

“Mutanen sun bayyana mana cewa ‘yan bindigan na dukan su saboda sun ki bada lambobin wayan ‘yan uwan su.

‘Yan bindiga sun kashe mutum 8

Muhammad ya ce ‘yan bindigan na yawan canja kudin fansan da suke bukata a biya da wurin da suke so a ajiye kudin wanda hakan ya sa ‘yan uwan mutanen da aka yi garkuwa da su suka dade wajen biyan kudin fansan.

“Mutum biyu din da suka gudu su ne kadai cikin mutum 10 din da aka kama da suka tsira da ran su.

“Yan bindigan sun ce a biya su naira miliyan 50 da farko sannan suka dawo kasa zuwa Naira miliyan 20 inda daga nan basu sake kira ba sai bayan kwanaki 10.

Muhammad ya ce ‘yan bindigan sun rika yi wa ‘yan uwan wadanda suka kama barazanar cewa za su kashe su idan har ba su yi gaggawan biyan kudaden ba. Amma rashin yanke hukuncin adadin yawan kudin fansan da ‘yan bindigan ke bukata na daga cikin dalilan da ya hana ‘yan uwan mutanen da aka kama biyan kudin fansan.

Mutanen da aka kashe

PREMIUM TIMES ta gano cewa mutane 8 din da ‘yan bindigan suka kashe duk maza ne.

Idi Mijin Hajia, Malam Zubairu, Murtala Nagoma, Umar Muhammad, Siddi Na umara, Habibu DanBala, Yahaya Attah da Zayyanu Nagoma na cikin mutanen da aka kashe.

PREMIUM TIMES ta yi kokarin magana da ‘yan uwan wadanda ‘yan bindigan suka kashe amma bai yiwu ba.

Sai dai wani mazaunin Zurmi Usman Kabiru na cikin mutanen da suka rika yin magana da ‘yan bindiga kan kudin fansa a madadin iyalin Idris Nagoma.

Kabiru ya ce iyalan Nagoma sun rasa mutum biyu Murtala da Zayyanu a hannun ‘yan bindiga.

Ya ce da suke magana da ‘yan bindigan sun gano cewa ‘yan bindigan za su kashe ‘yan uwan su saboda yadda basu mike tsaye sun fadi yawan kudin fansan da suke so ba.

Kabiru ya ce ‘yan uwan mutanen da ‘yan bindigan suka kama sun hada kansu inda suka samu maharan suka amince a biya su naira miliyan shida kudin fansan mutum 8.

“Sai dai bayan wani lokaci sai ‘yan bindigan suka kira inda suka sanar musu cewa sun kashe mutanen dukan su saboda mun ki mai da hankali wajen biyan kudin fansan.