Za mu fito da rahoton nazarin yi wa tsarin mulki kwaskwarima cikin Yuli – Omo-Agege

Shugaban Kwamitin Yi Wa Dokokin 1999 Garambarul da Kwaskwarima, Sanata Ovie Omo-Agege ya bayyana cewa a cikin watan Yuli za su gabatar wa Majalisar Dattawa rahoton kwamitin su.
Omo-Agege ya kara da cewa matsalar rashin isassun kudaden aiki da kwamitin ya fuskanta, ba ta zama wani kalubalen da ya kawo cikas wajen gudanar da ayyuka ga mambobin kwamitin ba.
Omo-Agege, wanda kuma shi ne Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, ya yi wannan bayanin a wani taron manema labarai da ya kira a ranar Litinin, a Abuja.
Ya ce duk da cewa kwamitin nazarin dokokin na aiki ne da kudaden da aka ware masa tun na cikin kasafin 2020, har yau karancin kudin bai kawo wa kwamitin wani ciksa ba.
“Har yau ba a ba mu ko sisi a cikin kasafin kasafin 2021 ba. Kenan har yanzu da kudaden da aka ware mana tun cikin kasafin 2020 mu ke aiki.
“Amma mu na fatan za a saka mu cikin dan kwarya-kwaryan kasafin da za a gabatar wa Majalisa kwanan nan, a saka mu a ciki.”
Ya ce kwamitin sa ya karbi makalu sama da 250 kuma duk an yi nazaarin su.
“Kwamitin mu ya sha tuntubar mutane da dama da kuma ganawa a shirye-shiryen zaman saurare a shiyyoyin kasar nan dukkan su.
“Batutuwan tattaunawar sun tashi daga 13 zuwa 16, wadanda su ka hada har da batun Kara wa Mata Kaso a Mukamai, kara shigar da mata a gwamnati, batun daddatsa iko daga tarayya zuwa jihohi da sauran su.”
Omo-Agege ya ce zaman sauraren ra’ayoyin da za a yi, zai rika gudana ne lokaci guda a shiyyoyin kasar nan baki daya, a ranakun 26 da 27 Ga Mayu.
“Za a yi zaman a santoci biyu na kowace shiyya. A Arewa ta Tsakiya za a yi a Jos da Minna.
“Sai Arewa ta Gabas za a yi a Gombe da Bauchi. Arewa ta Yamma kuwa za a zauna a Kaduna da Sokoto. Can a Kudu maso Gabas, za a zauna a Enugu da Owerri. A Kudu Maso Kudu kuwa, a Asaba da Bayelsa za a yi zaman sauraren. Sai a Kudu maso Yamma kuwa, a Akure da Lagos za a yi zaman.
“Bayan an yi zaman shiyya-shiyya an kammala, za a yi Babban Zaman Saurare na Kasa a Abuja, a ranar Alhamis, 2 Ga Yuni, da kuma Juma’a, 3 Ga Yuni.”
Omo-Agege ya ce za a yi zaman sauraren a Abuja domin a bai wa musamman manyan jami’an gwamnatin da ba su samu damar zuwa shiyyoyin su ba, su je su gabatar da ta su makalar a zaman Abuja.