ZAƁEN 2023: APC za ta iya faɗuwa zaɓe idan ba ta tashi tsaye ba -Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari ya ja kunnen jam’iyyar APC cewa idan ba ta yi da gaske ba, to ta na ji ta na gani jam’iyyar PDP za ta karɓe ragamar mulki a 2023, bayan cikar wa’adin mulkin sa.

Buhari na magana ne dangane da rikicin da manyan APC ke fama da shi na neman kasa shirya taron gangamin jam’iyya na ƙasa, domin zaɓen shugabannin jam’iyya.

Da ya ke tattaunawa da gidan talbijin na NTA a ranar Alhamis, Buhari ya yi tsokaci musamman ganin yadda rigima ke neman Kunno kai har taron gangamin na neman gagara.

Baya ga batun shugabancin jam’iyya, babban abin da ya dabaibaye APC shi ne batun ɗan takarar zaɓen shugaban ƙasa, wanda wasu ke neman a cimma yarjejeniyar fidda ɗan takara ba tare da yin zaɓen fidda-gwani ba.

Sai dai kuma Buhari ya ce shi ba shi gwani a cikin dukkan masu tsayawa takara. Don haka abin da doka ta ce a yi wajen fidda-gwani, shi za a yi kawai.

Buhari ya ce ya zama wajibi APC ta tashi tsaye domin bai wa ranar taron gangamin jam’iyya muhimmanci.

“Shi taron gangamin jam’iyya abu ne na wani ƙayyadajjen lokacin da doka ta gindiaya. Kuma tunda mulki bayan shekara huɗu ake canja shi, to ba zai yiwu a ce ba a yi taron gangamin jam’iyya ba a cikin wannan ƙayyadajjen lokacin ba. Saboda idan APC ta yi wasa, sai PDP ko wata jam’iyyar adawa ta karɓe ragamar mulki.

Buhari ya tunatar da yadda wasu gwamnonin da bai ambaci sunayen su ba, ya ce sun same shi da shawarar aikata wani abu da ba daidai ba a kan tsayar da ɗan takara, amma ya ce, “na ƙi yarda, saboda idan na amince, to jefa tsarin dimokraɗiyyar cikin halaka za su yi.”

Daga nan Buhari ya shawarci gwamnoni su bar doka da tsarin dimokraɗiyya su yi abin da ya dace kawai.