ZAƁEN 2023: Abin da Ubangiji na ya sanar da ni game da takarar zaɓen shugaban ƙasa – Gwamna Umahi

Gwamna Dave Umahi na Jihar Ebonyi ta bayyana cewa Ubangiji ya yi masa ilhamar cewa zai tsaya takarar shugabancin Najeriya a zaɓen 2023.

Haka ya furta yayin tattaunawa da ya yi da gidan talbijin na Channels, cikin shirin “Siyasa A Yau”.

Ya bayyana a shirin ne sa’o’i kaɗan bayan ya bayyana wa manema labarai a Fadar Shugaban Ƙasa cewa ya je ziyara ga Buhari kuma ya sanar da shugaban ƙasar cewa ya yi niyyar tsayawa takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023.

Umahi ya sanar wa Buhari aniyar sa ta fitowa takara ƙasa da kwana ɗaya bayan jigon APC Bola Tinubu ya sanar wa Buhari niyyar sa ta shi ma zai tsaya takara.

Zuwa yanzu dai masu neman fitowa takara daga APC mai mulki.

Umahi ya ce Ubangiji ya ce ya fito takara ne, amma kuma Ubangiji bai sanar da shi shin zai yi nasara ko ba zai yi ba.

“Ubangiji ya ce min na fito takarar zaɓen 2023. Amma fa bai sanar da ni ko zan yi nasara ko ba zan yi ba.” Inji Umahi.

“Matsawar Ubangijin ka ya yi magana da kai, ka yi magana da shi, to ai ka samu nasara babba. Kuma za ina ganin ni dai na samu kwanciyar hankali a rai na. Ba Ubangiji ne zai sanar da kai za ka ci zaɓe ko ba za ka ci zaɓe ba. Wannan kuma ƙudira ce ta Ubangiji.” Inji shi.

Da aka tambaye shi yadda zai kafsa zaɓen fidda-gwani da jiga-jigan APC, Umahi wanda bayan ya ci zaɓe sau biyu a ƙarƙashin PDP ya koma APC, cewa ya yi “Ubangiji me bayar da mulki ga wanda ya ga dama. Kuma shi kaɗai zai iya hana wanda ba a ƙaddare shi da zama shugaban ƙasa ba.

Yayin da Umahi wanda gwamna ne a ɗaya daga jihohin Kudu maso Gabas ya ce zai fito takara, shi ma Sanata Uzor Kalu ɗan yankin, kuma tsohon gwamnan Abia, ya ce zai fito takara, amma idan an damƙa takarar ga yankin Kudu maso Gabas.

Kalu ya ce zai fito takarar shugaban ƙasa, idan APC ta damƙa wa Kudu maso Gabas takara.

Yayin da zaɓen shugaban ƙasa ke ƙaratowa cikin 2023, Bulalar Majalisar Dattawa, Orji Kalu ya bayyana cewa zai fito takarar shugabancin Najeriya, idan har jam’iyyar APC ta damƙa takarar ga yankin Kudu maso Gabas, wato yankin ƙabilar Igbo.

Haka tsohon Gwamnan na Jihar Abia ya shaida wa Kamfanin Dillacin Labarai (NAN), yayin komawar sa Abuja, a filin jirgin sama na Nnamdi Azikwe, a ranar Talata.

NAN ta ruwaito Kalu na cewa ƙungiyoyi da dama sun nemi Kalu ya fito takarar shugabancin ƙasa, kuma sun bayyana cewa a shirye su ke domin su tabbatar cewa ya yi nasara a zaɓen 2023.

Sannan kuma an ga fastocin Kalu na neman takara an manna a kan titinan jihohin ƙasar nan da dama.

Yayin da ya ke yaba wa ƙungiyoyin da ke neman ya fito takara, mawallafin jaridun The Sun ya ce gani su ka yi shi ne ya fi cancanta, shi ya sa kowa ke rububin sa.

Ya ce tabbas shi ma ya ga fastocin sa sun cika garuruwa shi ya ƙara masa ƙwarin guiwar neman fitowa takara.

Sai dai ya ce shi zai yi biyayya ga jam’iyyar APC mai mulki. Saboda takarar sa na da sharaɗin cewa sai idan APC ta damƙa wa Kudu maso Gabas takara, sannan zai fito gadan-gadan.

“Ina mai godiya ga jama’a masu mammanna fastoci na a garuruwan Najeriya. Ni ban ce zan tsaya takara ko ba zan tsaya ba. Amma dai idan aka damƙa takara ga Yankin Kudu maso Arewa, to tabbas zan fito gadan-gadan.

“Amma dai na san cewa jam’iyyar mu za ta tsayar da ɗan takarar da zai haɗa kan Najeriya. Kuma dama hakan shi ne mafi muhimmanci ga ɗorewar ƙasar nan.” Inji Kalu.