‘Yan sanda sun ceto mutum 7 da aka yi garkuwa da su a Zamfara

A kauyen Dansadau dake karamar hukumar Maru jihar Zamfara ne ‘yan sanda suka ceto mutum bakwai da aka yi garkuwa da su.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara Mohammed Shehu wanda ya sanar da haka ya ce mutanen da aka yi garkuwa da su din ‘yan asalin kauyen Chibade ne dake karamar hukumar Rijau a jihar Niger.

Jihar Neja kamar yadda jihohin Zamfara, Katsina, Sokoto da Kebbi suke na fama da ‘yan bindiga da ke kisan mutane, mai da mutane ‘yan gudun hijira da sace-sacen dabbobi.

A wata takarda da PREMIUM TIMES ta samu ranar Lahadi Shehu ya ce jami’an tsaron ‘yan sanda tare da hadin gwiwar dakarun sojojin Najeriya suka ceto wadannan mutane a yankin Dansadau.

” Mutanen sun bayyana wa jami’an tsaron bayan an ceto su cewa a ranar 21 ga Faburairu ne ‘yan bindiga suka afka kauyen su a Chibade inda suka yi awon gaba da mutum bakwai zuwa wani wuri a dajin Dansadau.

” Bayan ceto wadannan mutane da jami’an ‘yan sanda da sojojisuka yi a dajin Dan sadau sai suka kai su asibitin Yariman Bakura dake Gusau domin a duba lafiyar su.

“Zuwa yanzu mutanen na hannun rundunar ‘yan sandan jihar Neja.

Kwamishinan rundunar ‘yan sandan jihar Ayuba ElkanaElkana ya ce rundunar ba za ta ja da baya ba wajen yaki da duk ‘yan bindiga a jihar.