‘Yan sanda sun bayyana sunayen matan da aka yi garkuwa da su a hanyar zuwa Coci a Katsina

Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta bayyana sunayen matan da ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su ranar Lahadi a jihar.
PREMIUM TIMES ta buga labarin cewa ‘yan bindiga sun yi garkuwa da wasu mata biyar a hanyar su ta zuwa coci a kauyen Mai Tsauni dake Gidan Haruna a karamar hukumar Kankara
Kakakin rundunar Gambo Isa ya ce ‘yan bindiga sun dira kauyen dauke da manyan bindigogi kirar AK-47 suka yi kan mai uwa dawabi.
Isa ya ce ‘yan bindigan sun ji wa faston cocin ‘New Life for All’ fasto Haruna rauni wanda a yanzu haka likitoci na duba shi a wani asibiti dake Kankara.
Ya ce ‘yan bindigan sun yi garkuwa da Rabi Isyaku mai shekaru 15, Rabi Saidu mai shekaru 36, Rabi Babba 49, Saratu Hadi mai shekaru shekara 27 da Nusaiba Shuaibu mai shekaru 13.
Isa ya ce ‘yan sandan dake Kankara sun kawo dauki kauyen sai sai kafin su iso maharan sun gudu.
Ya ce rundunar ta fara yin da bincike domin ceto mutanen da aka yi garkuwa da su.