‘Yan bindiga sun yi garkuwa da ‘yan Chana uku, sun kashe masu gadin su biyu a jihar Neja

A ranar Talata ne ‘yan bindiga suka yi garkuwa da ‘yan kasan Chana uku sannan sun kashe masu gadin su biyu a tashar Samar da wutan lantarki a jihar Neja.

Gwamnati na gina tashar samar da wutan lantarkin ne a kauyen Zungeru dake karamar hukumar Wushishi sannan kamfanonin CNEEC da SINOHYDRO ne ke aikin kwangilar aikin.

Wani da abin ya auku a idonsa ya ce ‘yan bindigan sun arce da wadannan mutane bayan sun yi bata kashi da ‘yan sanda a kauyen Gussase.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Wasiu Abiodun ya tabbatar cewa ‘yan bindigan sun harbe dan kasan Chana daya da wani dan Najeriya daya sannan suka arce da wasu mutum uku ‘yan kasan Chana da mutum daya dan Najeriya.

Abiodun ya ce ‘yan sandan dake aiki da ma’aikatan sun samu nasarar ceto ‘yan kasan Chana hudu yayin da suke bata kashi da ‘yan bindiga da suka yi inda a ciki akwai dan kasan Chana daya da dan Najeriya daya da aka harbe.

” Bayan arangamar da suka yi da ‘yan sandan sun gano cewa ‘yan kasan Chana mutum uku sun bace.

Abiodun ya ce rundunar ta fara farautar ‘yan bindigan da suka yi wannan mummunar abu domin ceto mutanen da suka yi garkuwa da su.