Yajin Aikin Likitoci: Za Mu Dauki Ma’aikatan Kiwon Lafiya Na Wucin Gadi – Gwamnatin Najeriya

Biyo bayan biris da gwamnatin Najeriya tayi na barazanar shiga yajin aiki da Kungiyar likitoci masu neman kwarewa NARD ta yi sati biyu da suka gabata, idan har gwamanti  ba ta biya musu bukatunsu da hakkokinsu ba, kungiyar likitocin ta tsunduma yajin aikin gargadi na kwanaki biyar.