Yadda ‘Yan bindiga suka kashe kwamishina Rabe Nasir a gidansa a Katsina

‘Yan bindiga sun kashe kwamishinan kimiyya da fasaha na jihar Katsina Rabe Nasir a cikin gidan sa ranar Alhamis da Yamma.

marigayi Nasir ya ta ba yin aiki da hukumar tsaro na SSS da EFCC a Abuja.

Nasir ya kuma wakilci shiyar Mani/Bindawa a majalisar tarayya daga shekarar 2007 zuwa 2011.

Daga shekarar 2015 zuwa 2019 Nasir ya zama maiba gwamna Aminu Masari shawara kan harkokin kimiyya da fasaha indabayan haka ya nada shi kwamishinan kimiya da fasaha.

Wani dan uwan Nasir ya bayyana wa PREMIUM TIMES cewa ‘yan bindigan sun kashe mamacin a gidansa dake Fatima Shema Housing Estate.

“Na je gidan bayan wani kawuna ya kira ni a waya sai na iske jami’an cirko cirko tsaye sun zagaye gidan sun hana kowa shiga.

Ya ce ‘yan bindigan da suka kashe Nasir sun kulle gawarsa a cikin ban daki.

“Wani cikin yan uwan mamacin ne ya tsinci gawar marigayi Rabe kulle a cikin bandaki.

A lokacin da ake rubuta wannan labari wata majiya ta tabbatar wa PREMIUM TIMES cewa gwamna Masari da tawagarsa na gidan marigayi Nasir.