Yadda rashin tsaro ke saka miliyoyin yara cikin matsalar matsanancin yunwa a Najeriya

Sakamakon binciken da hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta ƙasa ta gudanar ya nuna cewa mutane miliyan 2.7 ne suka rasa gidajen su a yankin Arewa maso Gabashin kasar nan.

Wasu daga cikin wadannan mutane na samun mafaka a sansanin ‘yan gudun hijira dake jihar Borno wasu kuwa sun tsallaka zuwa kasashen Niger da Kamaru.

Wasu cikinsu sun gudu zuwa jihohin Kaduna, Legas da Abuja.

A dalilin haka akwai akalla yara akalla miliyan 17 dake fama da matsanacin yunwa a kasar nan.

Hakan ya sa Najeriya ta zama ƙasa na farko a Nahiyar Afrika sannan ƙasa ta biyu a duniya dake da yawan yaran dake fama da yunwa.

Wata masaniyar abincin dake inganta garkuwar jiki Mary Makanjuola ta ce yunwa kan fara kama yaro tin Yana cikin mahaifiyarsa inda bayan ya an haife shi zata cigaba da zama a jikinsa idan ba adauki mataki a akai ba.

Bayan haka bincike ya nuna cewa yara ‘yan ƙasa da shekaru uku ne suka fi fama da matsanancin yunwa.

Wata mazauniyar sansanin ‘yan gudun hijira dake Munna garage a Maiduguri jihar Borno Fatsuma Bakari wacce ta kawo ‘yarta Salamatu mai shekara uku dake fama yunwa asibiti ta ce ‘yarta ta fada cikin wannan matsala saboda rashin samun abinci su ci.

Fatsuma ta ce tun da Boko Haram suka kawo wa kauyen su Dikwa hari a jihar Borno suka fara wahala inda har abincin da za su ci ke gagaransu.

” Da tsohon cikin Salamatu na gudo daga kauyen mu bayan Boko Haram sun kashe ‘yan uwa na biyar.

“Haihuwa ta shida inda na shidan na haifeta a hanya yayin da muke neman mafaka daga hare-haren Boko Haram.

“Tun da muka fara zama a sansanin nan muke wahalan cin abincike, bama sanin kula na kiwon lafiya .

Mun mai da ‘ya’yan mu mabarata

Wata mazauniyar sansanin ‘yan gudun hijira dake Silumnri Maimuna Musa dake sana’ar dinka hula ta ce yunwa ta kashe ‘ya’yan ta biyu.

“Haihuwa na tara biyu sun mutu sannan duk da sana’ar dinkin hulan da nake yi tuwo da garin kwaki kadai muke iya ci.

“A dalilin haka muke kira ‘ya’yan mu su fita waje su yi bata sannan duk abinda suka samo a barn muke haduwa muna ci.

Sakamakon rashin daukar mataki

Idan har ba an samar da abinci wa mutane ba mutanen dake yankin dake ake fama da rikici za su ci gaba da gama da yunwa.

Wakilin UN Matthias Schmale ya ce akalla yara ‘yan ƙasa da shekara biyar miliyan 1.4 dake Arewa maso Gabas za su yi fama da yunwa a shekaru masu zuwa.

Schmale ya ce yunwa na Yi wa rayuwar yara kanana barazana a jihohin Borno, Adamawa da Yobe.

Ya ce binciken da UN ta gabatar na kama da rahotan da aka gabatar kan samun abinci a Najeriya inda ya nuna cewa mutum miliyan 12.1 za su yi fama da yunwa nan da watan Disemba 2022.

Rahotan ya ce yunwan zai shafi jihohin 21 da Abuja sannan da mutum 416,000 mazauna sansanin ‘yan gudun hijira.

Schmale ya ce nan da ‘yan shekaru masu zuwa adadin yawan mutanen dake fama da yunwa zai karu zuwa miliyan 16.9 idan har ba a dauki matakan inganta rayuwar mutane ba.

Jami’ar lafiya dake Jami’ar koyar da kimiya da fasaha dake jihar Enugu Chidi Ezinwa ta ce tun farko yunwa da talauci na daga cikin matsalolin dake tauye wa yara hakinsu na samu ingantaciyar lafiya da ilimin boko.

Ta ce sannan yanzu abin ya karu da rashin tsaro inda Yara da dama ke fama da matsalolin yunwa.

Ezinwa ta ce kamata ya yi gwamnati ta mike tsaye ta shawo kan wadannan matsaloli domin inganta rayuwar mutanen kasar nan.