Yadda mutanen Kajuru suka dunguma fadar sarki Alhassan bayan sakin sa da ƴan bindiga suka yi

Mutanen garin Kajuru sun ɗunguma fadar maimartaba sarkin Kajuru Alhassan Adamu domin nuna farin ciki da murnar sako sa da ƴan bidiga suka yi.

Kamar yadda BBC Hausa ta ruwaito daga bakin Madakin Kajuru wanda ɗan sarkin ne, ya ce suna zaune kawai sai suka ga sarki ya shigo musu.

” Muna zaune ne fa kawai sai muka ji an yi mana sallama, ashe sarki ya dawo gida daga inda ƴan bindiga suka tsare shi kuma shi kaɗai.

Sai dai ya ce matan sa da sauran waɗanda aka sace su tare su 13.

Mutane sun yi cincirindo a fadar sarkin suna murnan sako shi da aka yi.

” Wannan abu ya tada mana hankali, sannan abin kunya ne ace rashin tsaro ya kai ga za a shigo gari a sace babban sarki haka a tafi da shi da iyalan sa. Gaskiya akwai matsalar rashin tsaro a jihar nan da kasa baki daya.

PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labarin yadda aka sace sarkin Kajuru tare da iyalansa da wasu 13 ranar Lahadi.