Yadda kakkausan kalaman Basaraken Yarabawa ya ja masa sa-in-sa da shugabannin Ndigbo

Ƙurar da Basaraken Oluwo na Masarautar Igbo, Abdulrasheed Akanbi ya kakkaɓa a kan ɗaukacin ƙabilun Igbo masu neman a ba su shugabancin ƙasa a 2023, ta na ci gaba da tashi, har yau ba ta lafa ba.
Saboda duk da Ndigbo ta mayar masa da martani, har yau Akanbi na nan a kan ra’ayin sa cewa lokacin bayar da mulki ga ɗan ƙabilar Igbo bai yi ba tukunna, har sai sun ƙara ƙoƙarin jan sauran ƙabilun ƙasar nan a jika sun karɓe su hannu bibbiyu, kamar yadda sauran ƙabilun suka karɓi Igbo hannu bibbiyu a yankunan su.
Sai dai ya musanta zargin da ake yi wai ya ce ɗan ƙabilar Igbo ba zai taɓa yin shugabancin Najeriya ba.
Ya jajirce dai cewa tabbas idan har Igbo na son a ba su shugabancin ƙasa, to tilas sai sun yi wa ‘yan sauran ƙabilun ƙasar nan runguma, ba ƙyamata ko hantara ko wani zare idanu da buɗe idanu ba.
Akanbi ya ce matsalar Igbo ita ce sun nuna tsanar sauran ƙabilu ba su rungumar su, musamman waɗanda ke zaune a jihohin Igbo da aka mayar saniyar-ware, alhali sauran ƙabilun ƙasar nan sun rungumi Igbo hannu bibbiyu a jihohin su da Igbo ɗin ke zaune su na kasuwanci.
Basaraken ya mayar wa ƙungiyar masu kishin Igbo Zalla, Ndigbo raddi a ranar Laraba cewa misali, sai ɗaukacin Igbo su haɗa kai sun daƙile zaman-gida-dirshan da tsageru da ‘yan iskan ƙabilar Igbo su ka ƙaƙaba a wasu jihohin Kudu maso Gabas.
Sannan kuma basaraken ya zargi Igbo da hana sauran ƙabilun ƙasar nan mallakar filaye da kantina a kasuwar Anacha.
Ya ce amma ƙabilar Igbo da ke zaune a sauran biranen ƙasar nan a Kudu ko a Arewa, su na samun damar sayen filaye, gidaje ko mallakar kantina a kasuwannin garuruwan da su ke harkokin su.
“Babu wani ɗan Najeriya da zai ji ya na zaune ƙalau a ƙarƙashin shugaban da ƙabilar sa ke danne wa sauran ‘yan Najeriya wani haƙƙi ko ‘yancin su.”
Haka basaraken ya bayyana a cikin wata sanarwar da Kakakin Yaɗa Labaran sa Alli Ibraheem ya sa wa hannu, kuma ya raba wa manema labarai.
A raddin farko da Ndigbo na farko, sun zargi basaraken ya furta kalaman ruruta rarrabuwar kai.
Sanarwar da Sakatare Janar na Ƙungiyar Ndigbo na Duniya Arankatakaf, mai suna Chiedozie Ogbonnia ya fitar kuma ya sa w hannu, ya ce basaraken na Yarabawa na buƙatar a yi masa ƙarin ilmin sanin “sigogin kalaman fada.”
Sun ce ya je ya ɗauki darussa wurin mashahuran sarakunan Yarabawa Iran n su Oba Adeyeye Ogunwusi, Oni na Ife.
Ya kuma ƙaryata zargin cewa ana tauye haƙƙin sauran ƙabilun Najeriya da ke zaune a jihohin Igbo.
Shi dai basaraken ya ce ya na so ya na mutumin Kano ko na Legas ya na sayen filaye ko kantina a garuruwan Igbo.
“Kuma ina ƙalubalantar Gwamnan Anambra ya naɗa Bayarabe ko Bahaushe cikin kwamishinonin sa, kamar yadda aka yi a Legas, Osun, Kano, Kaduna da Sokoto.”