Yadda Ƴan bindiga suka yi garkuwa da manoma biyu suka bukaci a biya naira miliyan 10 kuɗin fansa

Ƴan bindiga sun yi awon gaba da wasu manoma biyu a kauyen Ileogbo dake jihar Osun.
Maharan sun yi garkuwa da Samuel Oladotun da Fashola Tobiloba a cikin makon jiya a lokacin da suke dawowa daga gonakinsu.
Wani jami’in tsaron da bayaso a fadi sunnan sa saboda rashin izinin yin magana da manema labarai ya ce a wannan rana ‘yan bindiga sun tare wani mota dake dauke da manoma bakwai a hanyar Oke Osun dake Ileogbo daga ganin haka sai suka dira suka fece da da gidu, sai dai biyu ba su yi arce wa ƴan bindigan sun kama su.
Wani daga cikin makusancin iyalan manoman da aka sace ya ce maharan sun bukaci a biya naira miliyan 10 kafin su saki manoman da suka kama.
Bayan haka kwamandan Amotekun Amitolu Shittu ya tabbatar da haka sannan ya ce jami’an su na farautan maharan a dajin Ileogbo domin ceto manoman da aka yi garkuwa da su.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Yemisi Opalola ta ce rundunar za na gudanar da bincike domin ceto wadanda aka yi garkuwa da su.
Wannan shine karon farko da ‘yan bindiga suka yi garkuwa da mutane a shekarar 2023.
Jihar Osun na daga cikin jihohin Kudu Maso Yammacin Najeriya da hare-haren ‘yan bindiga ya yi tsanani. Hanyoyin Gbongan zuwa Ibadan, Ilesa zuwa Osogbo na daga cikin wuraren da maharan ke garkuwa da mutane akai akai.
A Ilesa da Osogbo maharan sun fi yin garkuwa da turawa baki dake hako ma’adinai a yankin.