Wasu Sanatoci uku sun ƙara ficewa daga PDP zuwa APC

Raba a Facebook

Tura zuwa Twitter

Shugaban majalisar dattijai Sanata Ahmad Ibrahim Lawan ya sake karanto wasikun wasu Sanatoci uku da suka sauya sheƙa daga PDP zuwa APC a zauren majalisar a zamanta na yau Laraba.

Ƴan majalisar sun haɗa da Sanata Sahabi Yau (Sanata mai wakiltar Zamfara ta Arewa), Sanata Lawwali Hassan Anka (Sanata mai wakiltar yankin Zamfara ta yamma), Sanata Peter Nwaoboshi (Sanata mai wakiltar Delta ta Arewa).

Ko a jiya Talata ma shugaban majalisar ya karato takardar sauya sheƙar wani Sanata daga jihar Zamfara Sanata Hassan Nasiha da ya fice daga APC. Sai dai