Wasu na zargin cewa yarjejeniyar da ta tanadi dunkule Najeriya a matsayin kasa guda a shekarar 1914 ta kare bayan shekaru 100. Shin hakan gaskiya ne? Binciken DUBAWA

Kwanan nan, kuma na tsawon shekaru 10 yanzu ake mahawara a kan hadin kan Najeriya da kuma yiwuwar cigaba da kasancewarta a matsayin kasa daya dunkulalliya. ‘Yan siyasa da kwararru a fanin illimi na ta bayyana dalilan da ke tsokaci kan yadda har yanzu kasar ke fama da rashin hadin-kai. Ga mutane da yawa ciki har da masu bincike, da masu sharhi, matsalar Najeriya ita ce hade yankunan arewaci da na kudancin da Burtaniya ta yi da karfi da yaji. Abin da yanzu ake wa lakabi da kuskuren 1914, hadewar da kuma ake gani ita ce mafarin gurguncewar kasar.

Yayin da Burtaniya (A karkashin jagorancin Lord Frederick Lugard) ke da nata dalilin na hada yankunan biyu, da yawa ba su fahimci dalilin hadewar ba, domin a ganinsu ya kamata a dare kowa ya yi hanyarsa. Wannan ra’ayi na samun karbuwa sosai musamman masu ra’ayin ‘yan aware, wadanda ke cewa dama can wa’adin shekaru 100 ne aka debawa hadewar.

Kwanan nan, da yawa daga cikin ‘yan awaren na cewa a shekarar 1914 lokacin da aka hada yankunan biyu akwai tanadin darewa a cikin yarjejeniyar da ya samar da hadakar, wanda ya sami amincewar kowani yankin da ke cikin yarjejeniyar, kuma wa’adin shi a yanzu haka ya cika.

Daya daga cikin masu irin wadannan maganganun shi ne Konye Obaji Ori wanda a shekarar 2013 ya rubuta cewa wa’adin dokar Birtaniya ta 1914 ta cika ranar 31 ga watan Disembar wannan shekarar, kuma kafin a kara wa’adin dole sai an zauna kowane bangare ya amince a yi ko kada a yi. A cewarsa “wa’adin takardar da ya hada Najeriya a matsayin kasa guda zai cika. Za’a iya kara wa’adin ko kuma a yi watsi da dokar shekarar ta 1914 na masu mulkin mallakar Burtaniya. Najeriya na iya cigaba da kasancewa yadda ta ke ko kuma ta dare zuwa kananan yankuna masu cin gashin kansu.

Haka nan shi ma Tony Nnadi, lauya kuma babban sakataren kungiyar Movement for New Nigeria ya hakikance a shekarar 2014, cewa daga wannan shekarar babu sauran kasar da aka sani a matsayin Najeriya saboda wa’adin wannan hadakar ya kare, kuma kowace kabila na da ‘yancin ballewa ta zama kasa mai cin gashin kanta.

“Najeriya yadda aka santa ta kare. Yadda za a bayyana shi a takaice ke nan,” a cewarsa. Ya kara da cewa hadewar bai faru kai tsaye ba, akwai abubuwa da yawa da suka faru kafin aka kaiga yarjejeniyar ta 1914 dan haka akwai bukatar warware abubuwa da yawa kafin a kai ga kammala batun hadewar.

“Burtaniya ba ta sami kasar cikin dare guda ba, a shekarar 1861 aka kulla yarjejeniyar Legas sannan wasu wuraren turawan sun ci su da yaki ne sai daga baya suka kulla yarjeniyoyi a wurare daban-daban kafin suka fara hadakar. Wannan ya fara tun a shekarar 1906. A 1906 suka tattara duk arzikin da suka samu wato ruwayen da ke da ma’adinan man fetur da kuma Legas suka hada su waje guda suka kira su yankin kudanci. A shekarar 1914 suka kammala komai a takarda guda daya wanda ya zama abun da muke kira hadewa ko kuma amalgamation a turance.”

Paul Eric ma ya bayyana wannan ra’ayin a shekarar 2016 lokacin da ya rubuta cewa “hadewar da aka yi a shekarar 1914 yarjejeniya ce aka kula. A bayyane yake cewa a dokokin kasa da kasa duk wata yarjejeniyar da ba’a tantance ranar da zata kare ba, wajibi ne a daina amfani da ita bayan shekaru 100. Bisa la’akari da haka a idon doka, kasar ba ta halata ba.

To sai dai Paul Eric kadai ne ke da wannan ra’ayi domin marubucin wannan binciken ya tantance rahotanni da dama dangane da hadewar Najeriya kuma babu inda aka ce yarjejeniya ce aka kulla.

To amma Hadewar (amalgamation) Yarjejeniya ce aka kulla?

Da farko dai babu wani bincike, hatta rahoton da Lord Lugard ya rubuta dangane da hadewar yankunan arewaci da kudancin Najeriya da ma gudanar da ita tsakanin 1912-1919 (Wanda aka gani a dakin ajiyan litattafai na kasa da ke jami’ar Ibadan), da ke nuna cewa an kulla wata yarjejeniya. Ma’anar yarjejeniya ita ce tattaunawa dan cimma matsaya ko kuma sanya hannu kan kwantiragi tsakanin hukumomin siyasa biyu ko fiye (Kamar jihohi ko kasashe masu cin gashin kansu) a hukumance a gaban wakilan da kowani bangare ya amince da su, wadanda kuma suka sami amincewar hukumomin dokar kasa. Idan dai haka ne, babu wata hujjar da ta tabbatar wannan ya faru.

Sai dai a batun hadewar, gaskiyar abun da aka tabbatar ya faru shi ne shugabanin mulkin mallakar Burtaniya suka hada yankunan da ke karkashin su domin samun saukin tafiyar da ayyukan gudanarwa da wadanda suka shafi tattalin arziki.

Da ya ke tsokaci dangane da wannan batun, farfesa a sashin tarihi na jami’ar Ibadan Farfesa Rasheed Olaniyi ya bayyana irin dalilan da ke kai ga hadewar yankuna su zama kasa guda. “Dunkule kasa na iya daukar sufofi iri-iri. Wadansu sukan dunkule kasar da ke da banbance-banbance ta hanyar yaki, daga baya a shirya a zauna lafiya. Wata suffa kuma zata iya kasancewa ta mulkin mallaka kamar yadda muke da ita a Najeriya sannnan kuma akwai yarjejeniya ta hanyar diflomasiyya. To amma a Najeriya babu wata yarjejeniya, mulkin mallaka ce.

Burtaniya ta ga cewa zai fi mata sauki wajen gudanarwa da kuma shirya kasafin kudi da ma sauran dawainiyar tafiyar da tattalin arzikin Najeriya a karkashin mulkinta a wancan lokacin. Wadannan ne dalilai ukun da ya sa aka hada yankunan a waje guda. Tabbas, Burtaniyar ta yi haka ne domin ta rika cin gajiyar tattalin arzikin kasar ba wai dan ta inganta rayuwan jama’ar kasar ba. Na yi amfani da kalamar jama’a(peoples) saboda banbancin kabila da al’adu da sauransu.”

Masana tarihi Mathias Isiani da Ngozika Obi-Ani su ma sun ce ba shakka al’adun yankuna biyu sun sha banban, amma duk da haka a shekarar 1914 Lord Lugard ya hada su, abin da ya nuna cewa shawara ce da gwamnatin mulkin mallakar Burtaniyar da yanke da kanta ba tare da shawarwar kowani yanki daga cikin wadanda ta hada waje gudan ba.

Lugard da kan shi ya fayyace hakan a rahoton shi da ake yawan amfani da shi

A bayyane yake cewa kasa mai fadi kamar Najeriya wadda ke da fadin 332,400 square mile, kuma layin jirgin kasa daya tilo ya hada yankin arewaci da kudanci da hanyoyin ruwan Niger marasa tabbasa kuma ko daya babu wata hanyar sadarwa – dole sai an raba shugabanci tsakanin hukumomi biyu ko fiye wadanda ke dogaro da juna a karkashin gwamnati a tsakiya. Matsalar da ta bayyana kanta da farko ita ce yawan gwamnoni da ikonsu da kuma dangantakarsu da sassa daban-daban da kuma kananan hukumomin da ke karkashinsu a yankunan kasar baki daya. Sannan kuma akwai jagorancin sassan jiragen kasa da dakarun sojoji wadanda suka fito daga kusan kowani yanki a Najeriyar. Akwai kuma ayyuka da tsarin mulkin nan gaba na majalisu, da hade dokoki da ka’idojin da aka gindaya bisa wadannan dokoki da zartarwa da sauran umurni, da tsarin shari’a da hanyoyin karbar haraji da kuma yadda za’a yi amfani da kudaden shiga ta yadda za su taimaki kasa baki daya ba tare da janyo kishi ko fada tsakanin yankunan ba. Akwai kuma sajewa da manufofin ‘yan kasa – Wadannan da wadansu kananan matsaloli suka kasance wajibi a shawo kansu ta hanyar hadewa ko da kuwa ta yaya sannan kuma ya kasance a mataki na dindindin……

Akwai tanadin da ya ce wa’adin hadewar zai kare?

Da muka binciki takardu da litattafai, muka kuma kuma saurari bayanan masana tarihi da masu sharhi, babu wanda ya ce mana wai akwai tanadin da ya ce kasar ta dare bayan ta cika shekaru 100. Masanin tarihi Farfesa Olaniyi Rasheed y ace a ra’ayinsa babuwa wani wa’adi da aka sanya.

“Babu wani wa’adi, ko da kuwa na shekaru 100. A gani na idan ana neman tayar da zaune tsaye domin a dare ko wani abu makamancin haka, za’a yi ta farfaganda iri-iri. Za’a yi ta kawo labarai daban-daban, dan haka ba wani abu kamar shekaru 100,” a cewar farfesa Rasheed Olaniyi

“Babu wani abu kamar yarjejeniya, turawan mulkin mallaka suka tilsata mu. Hasali ma sai a shekarar 1947, ‘yan siyasar Najeriya suka taru suka tattauna wannan batun a karon farko, lokacin ne aka girka majalisar dokoki. Bayan nan ne suka sake haduwa a shekarun 1953, 1954 da 1955. Sun hadu a lokuta daban-daban a Legas. Akwai kuma taron da aka yi a Ibadan, da wanda aka yi a Landan inda suka tattauna batutuwan da suka shafi Najeriya dangane da mulkin mallakar da gwamnatin jihohi. Dan haka basu hadu kafin 1947 ba. Wannan ne karon farko da majalisun dokoki ukun wadanda suka hada da na lardunan yammaci, arewaci da gabashi suka hadu.

“Babu wata yarjejeniyar hadewa ta 1914. Babu wani abu mai kama da haka. Wa ya wakilci waÜ kuma a ina? Wadannan ne tambayoyin da ya kamata a yi. Wa ya wakilci kudu ko arewa a wancan lokacin? Idan ma akwai wani abu haka, turawan mulkin mallaka suka tilasta domin na daya, akwai banbance-banbance a irin ma’adinan da kowani fanni ya mallaka a wancan lokacin. Dan haka akwai bukatar daidaita kasafin kudi dan samar da kayayyakin more rayuwar da za su taimaka wajen amfani da tattalin arzikin kasar. Akwai bukatar samar da layin (dogo) jirgin kasa, da hukumar kwastom da kuma kudaden gudanar da ayyukan wasu fannonin gwamnatin wancan lokacin.”

A Karshe

Daga bayanan da muka samu hatta rahoton Lord Frederick Lugard babu wata hujjar cewa hadewar yankunan Arewaci da kudancin Najeriya a 1914 yana da wa’adin shekaru 100 duk kuwa da yadda masu sharhi ke tayar da jijiyar wuya suna zargin hakan a cikin kasar.

Haka nan kuma, babu wata yarjejeniyar da shuwagabannin yankunan suka sanyawa hannu, turawan mulkin mallakar Burtaniya ne kawai suka hada kasar domin samun saukin gudanar da ayyu