Video: Tabbasa Ƴan-Bindiga na ci gaba da shan luguden wuta a Zamfara- Gwamna Matawalle

Raba a Facebook

Tura zuwa Twitter

Gawmnan jihar Zamfara Muhammad Bello Matawalle ya tabbatar da cewa matakan da suke ɗauka na ci gaba da samun tagomashi a ƙoƙarin su na kawo ƙarshen hare-haren ƴan ta’adda a jihar, ya ce Ƴan Bindiga na ci gaba da shan luguden wuta a hannun Sojoji a jihar.

Gwamnan ya bayyana haka ne cikin wani Bidiyo da Hausa Daily Times ta samu, inda ya yi jawabi bayan Sallar Juma’a a wani masallaci a birnin Gusau

Gwamna Bello Matawalle, ya ce babu shi babu sauran sulhu da ƴan ta’addan domin ya yi duk abin da zai iya na daidaitawa da su amma sun ƙi. Ya ce abin da ya rage tsakanin shi da su shine “Tura su wurin Ubangiji sun amsa tambayoyi”.

Ya nemi al’ummar jihar da su ƙara haƙuri da halin matsi da suke ci bisa matakan da aka ɗauka, yana mai cewa an yi hakan ne somin dawo da zaman lafiya a jihar ta Zamfara.

Ga Cikakken Bidiyon Jawabin https://youtu.be/MVt9wk3WMSE