TUN BA A KAMA MULKI BA: Dattawan Ohanaeze Ndigbo sun ragargaji Tinubu, cewa ya fara nuna m’wa Igbo wariya

Kungiyar Kare Muradun Ƙabilar Igbo Zalla, wato Ohanaeze Ndigbo, ta ragargaji zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, Bola Tinubu har da kiran sa mai tsananin nuna ƙabilanci kan ƙabilar Igbo, saboda ya ƙi saka sunan ko da ɗan ƙabilar su ɗaya a cikin kwamitin karɓar mulki daga hannun Buhari.
Kwanan nan ne Tinubu ya kafa kwamitin mutum 14 waɗanda za su tsara karɓar mulki daga hannun Shugaba Muhammadu Buhari zuwa ga Bola Tinubu, wanda za a rantsar a ranar 29 Ga Mayu.
A cikin jerin sunayen waɗanda PREMIUM TIMES Hausa ta gani, babu ɗan ƙabilar Igbo a ciki ko ɗaya.
Da ya ke wa Tinubu raddi, Mataimakin Shugaban Ohanaeze Ndigbo, Damian Okeke-Ogene, ya zargi Tinubu da nuna zunzurutun ƙabilanci, kamar yadda kafafen watsa labarai su ka ruwaito.
“Ƙabilancin tsoron ƙabilar Igbo ya yi katutu a jini da jijiyoyin Tinubu, saboda ga shi nan a fili ya nuna tunda babu ƙabilar Igbo ko ɗaya a cikin kwamitin karɓar mulki da ya kafa. Yanzu mun gane ya na ƙoƙarin jangwalo tsohon miki ne kawai.
“Ya gaji wannan ƙabilanci da ƙiyayya kan Igbo da Buhari, musamman shi ma Tinubu ya ce zai fara mulki me daga inda Buhari ya tsaya.”
“Mene ne zai ci gaba wanda Buhari ya fara in banda mayar da ƙabilar Igbo saniyar ware da nuna masu ƙiyayya?” Inji shi.
“Mu fa har yanzu ba mu amince da Tinubu a matsayin shugaban ƙasa mai jiran gado ba. Ohanaeze ba ta yarda da sakamakon zaɓen Tinubu ba. Don haka duk abin da ya ke yi, ya na yi ne don kan sa kwai.
“Abin da kawai mu ka sani shi ne, masu son su raba Najeriya ba za su yi nasara ba.
“Har yanzu Ohanaeze ba ta amince da nasarar Tinubu ba. Saboda duk gidan da ba a gina kan nagartattun tubali ba, to rugujewa zai yi. Shi ya sa mu ba ma gaggawar yarda da nasarar Tinubu.”