TSARO: An kashe ‘yan sanda uku da wasu mutane 18 a cikin makon jiya a Najeriya

Akalla mutum 21 ne suka rasa rayukansu a cikin makon jiya a Najeriya. Daga cikin mutum 21 din da aka kashe akwai ‘yan sanda uku da wani basarake daya.
Mafi yawa daga cikin mutanen da aka kashe ‘yan yankin Arewa maso Yamma sai kuma yankin Kudu maso Yammacin kasar nan.
Jihar Zamfara
Akalla mutum 9 ne aka kashe sannan da dama sun rasa gidajen su a dalilin harin da ‘yan bindiga suka kai ranar Lahadi a karamar hukumar Tsafe.
Kauyukan dake kananan hukumomin Tsafe a jihar Zamfara da Faskari dake jihar Katsina na daga cikin wuraren da gogarman ‘yan bindiga Adamu Aleru ke yawan kai wa hare-hare.
Wani mazaunin Tsafe Salisu Sabo ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa kauyukan Magazawa, Kajera, Unguwar Dan Halima, Unguwar Rogo, Unguwar Ango, Kurar Mota da Kauyen Kane na daga cikin kauyukan da aka kai wa hari.
Jihar Jigawa
Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa ta bayyana cewa an kashe ma’aikatan ta guda biyu kuma an yi garkuwa da sirikin wani babban dan kwangila Haruna Maifata a jihar.
An yi garkuwa da Ma’aru Abubakar a cikin gidan sa dake kauyen Kwalam a karamar humumar Taura.
Jihar Ogun
A ranar Litini din makon jiya wasu mutane suka cinna wa wani basarake da ‘ya’yan sa maza uku wuta suka kone ƙurmus a jihar Ogun.
Sarkin kauyen Agodo dake karamar hukumar Ewekoro Ayinde Odetola ya gamu da ajalinsa bayan wasu mutane sun afka fadarsa.
Bayn haka shima sifeto Omolayo Olajide dake aiki da rundunar ‘yan sandan jihar ya rasu yayin da suke bata kashi da ‘yan bindiga ranar Talata.
Kakakin rundunar Abimbola Oyeyemi ya ce ‘yan sandan sun kashe ‘yan bindiga biyu a awannan rana.
Jihar Osun
Mutum biyar ne suka rasu a dalilin rikicin da aka yi tsakanin wasu ‘yan kungiyar ‘yan asiri da masu kwacen fili da aka yi a Ilesa.