TSAKANIN SARKIN KANO/MASARAUTAR KANO DA AIR PEACE: Ba mu yi wa sarki laifi ba – Martanin Air Peace

Air Peace ya maida wa masarautar Kano martanin cewa bai yi wa sarki Aminu Bayero na Kano laifi ba kamar yadda masarautar ta ke zargi.

Air Peace ya ce dama jirgin da sarki ya biyo daga Banjul iyakarsa Legas. ” Kuma ko a lokacin da Isa Pilot ya kira shugaban kamfanin jirgin saman Air Peace jirgin Legas zuwa Kano ya gama lodi zai tashi kenan. Sarki ya kira ya ce a dakatar da ita na awa daya.

Sai dai kuma duk da haka fadar sarki Aminun Kano ya ce kamfanin sun yi wa sarki wulakanci ne saboda haka su aiko da takardar ban hakuri ga masarautar Kano ko kuma wankin hula ya kai su dare.

Masarautar Kano ta ce da gangar aka yi wa sarki Aminu da tawagarsa wulaƙanci a filin jirgin saman Legas ɗin.

Dalilan da su ka harzuƙa Masarautar Kano neman afuwar Air Peace a cikin kwanaki uku

Ɗaya daga cikin ‘ya’yan Sarki a Kano, mai suna Isa Bayero, ya bai wa kamfanin zirga-zirgar jiragen sama na Air Peace wa’adin sa’o’i 72 cewa su nemi afuwar tozarta Sarkin Kano Aminu Ado-Bayero da jirgin ya yi, har ya haddasa wa sarkin da tawagar sa ɓata lokaci.

Bayero wanda kawun sarki ne, ya bayyana wannan sanarwa ce a ranar Asabar, yayin da ya ke magana da wasu manema labarai a Kano, ciki har da wakilin PREMIUM TIMES.

Ya ƙara da cewa tilas kuma kamfanin Air Peace ya amsa laifin da ya yi na rashin tashi lokacin da aka ƙa’ide masa, wanda ya ce hakan ya haddasa ɓata lokaci da jinkiri ga Sarkin Kano, wanda aka bar shi a tashar jirage ta Legas zaman dirshan ɗin jirgi.

Tun da farko dama Bayero ya rubuta takardar koke da ƙorafin laifin da ya ke iƙirarin Air Peace sun yi wa Sarki Aminu ga Hukumar Kula da Sararin Samaniyar Najeriya (NCAA) domin ta yi hukuncin da ya dace a kan kamfanin.

Isa, wanda aka fi sani da Isa Pilot, ya ce Air Peace ya haddasa masu ɓata lokacin awa ɗaya a tafiyar dawowar su daga Banjul a Gambiza zuwa Legas. Sannan kuma ya ce an hana ‘yan tawagar sarki shiga jirgin da zai tafi Kano.

Isa ya ce ‘yan rakiyar Sarki sun isa Legas minti 30 kafin lokacin tashin jirgi.

Ƙorafin Isa na ƙunshe iƙirarin cewa ya kira Shugaban Air Peace Allen Onyema, cewa ya sa a jinkirtar da jirgin da zai tafi Legas da safe saboda batun Banjul.

“Amma sai ya ƙi yin hakan, ya ce ba zai yi haka ba. To ni a ƙashin kai na na ɗauki abin da aka yi a matsayin cin fuska ha Mai Martaba Sarkin Kano da mutanen Kano baki ɗayan su.” Inji Isa Bayero a cikin wasiƙar ƙorafin.

Ya shaida wa manema labarai cewa zai ci gaba da yin magana har sai lokacin da Allen Onyema ya bai wa Sarkin Kano haƙuri.

Bayero ya ƙaryata iƙirarin da Air Peace ya yi, inda ya ce sun yi wa sarkin tayin wani jirgin daban, wanda zai ɗauke Sarki da tawagar sa daga Abuja zuwa Kano, cewa ƙarya ce ba a yi hakan ba.

“Ni da kai na na nemi alfarmar Sarki ya bi wanan jirgi daga Abuja zuwa Kano, amma Air Peace su ka ce min ya cika.” Inji Isa Bayero.

Ya ce a ƙarshe ma daina ɗaukar kiran lambar sa Air Peace ya yi.

“Mun rigaya mun sayi tikitin jirgin, don haka ban ga yadda za a yi su tashi su bar mu ba. Wannan cin mutuncin Sarki da al’ummar Kano ne baki ɗaya.

“Saboda haka ina bai wa Air Peace wa’adin sa’o’i 72 ya bada haƙuri ga Sarki a cikin wasu jaridun ƙasar nan masu fitowa kowace rana. Idan ba haka ba kuma, za mu ƙara gaba har sai mun dangana inda za a gyara wa Air Peace zama.” Inji Isa Pilot, wanda ya yi kurarin cewa shi ma tsohon diraban jirgin sama ne, har ma ya taɓa tuƙa shugabanni biyar.

A ƙarshe ya nuna bai damu ba idan Air Peace ya daina zuwa Kano, domin a cewar sa, tun kafin a kafa Sir Peace Kanawa ke zirga-zirga a jiragen sama.