TSADAR RAYUWA: Yadda wake ke keman ya gagari talakan da ke noma shi

Yayin da Hukumar Abinci ta Duniya (FAO) ta fitar da rahoton cewa farashin kayan abinci ya yi tashin-gwauron-zabi wanda bai taba yin irin tsadar ba tsawon shekaru 11, wani bincike da PREMIUM TIMES HAUSA ta yi, ya nuna cewa kayayyakin abincin da akasari talakawa ke ci domin rayuwar yau da kullum, su na neman su gagari talakawa.

Wake, masara, shinkafa da sauran kayan abinci sun tsawwala tsadar da ta kai yawancin magidanta sai dai su riƙa auno wanda za su iya ci a kullum. Saboda ba kowa ke da sukunin iya sayen kayan abincin da zai iya aniyewa ba.

Wakilin mu ya fara da farashin wake a cikin Kano, inda kwano ɗaya ya kai naira 1,200. Magidanta da ba su iya aunar kwano ɗaya a rana ɗaya, sai dai a riƙa auno ƙaramin gwangwanin madarar ruwa a kan naira 80.

“Bara kamar yanzu har naira 500 na kan tuƙa mota na je kasuwar Ladin Makole (Lord Macauley) na auno ko kwano nawa na ke so. Amma ka ga bana ko a can ya kai naira 1,000 ko ma ya haura.” Haka wani mai suna Alhaji Sani Mohammed ya shaida wa wakilin mu.

Wani mai suna Ali, mutumin Badume, cikin Karamar Hukumar Dawakin Tofa, ya tabbatar wa wakilin mu a ranar Larabar nan cewa, “a gaba na na ga ana sayar da babban kwanon awon ‘bangajin Sasakawa’ ɗaya na wake kan naira 1,500. To ka ga mu da ke noma waken nan a ƙauyukan mu, ba za mu iya cin sa yanzu haka da rani ba. Dama kuma ɗan wanda mu ke nomawa da damina, tun kafin kaka ta yi nisa mu ke cinye shi.”

Wani bincike da wakilin mu ya yi a Garki, cikin Jihar Jigawa, ya gano cewa a can ana sayar da wake kwano ɗaya naira 1,000. To sai dai kuma waken daraja-daraja ne, wani bai kai wani nagarta ba.

PREMIUM TIMES HAUSA ta gano cewa ana sayen buhun niƙaƙƙen garin masara buhu ɗaya har naira 26,000 mai cin kwano 40.

Haka kuma a Kano akwai shinkafar waje, wadda aka hana shigo da ita, amma ana sayar da buhun ta mai cin kwano 17 da rabi, naira 25,000. Shi kuma buhun shinkafar gida, wadda ake kira mai tsakuwa naira 22,000.

Wani bincike da wakilin mu ya yi, ya fahimci yawancin gidajen marasa galihu da ke cin shinkafa da wake da mai da yaji, a yanzu haka ya gagara.

Da yawan gidaje an koma cin ɗanwaken fulawa da rana, ko kuma a yi wainar fulawa ɗin, a bai wa yara su riƙa dangwalawa da mai da yaji, madadin abincin rana.

Gidaje da yawa an daina ɗora girkin abincin dare. “Abin da wasu da dama ke yi, idan aka dafa na rana, to ba a ci a ƙoshi har a yi ‘hani’an’. Sai dai a ɗan ci a bi shi da ruwa, a rage sauran da za a ci da dare.

“Saboda ka ga dai ga tsadar abinci, ga kuma tsadar gas. To yawancin gidaje da gawayi su ke girki. Kuma aiki ne mai wahala. Sai su haɗa abincin rana da na daren duk da rana. Amma dai maganar gaskiya ba wai ƙoshi fa ake yi ba.” Inji wata mai fama da yara ƙanana a gaban ta, wadda ta ce wa wakilin mu kullum sai ta fita ta nemo kuɗin da za a yi abincin gobe.

“Wallahi ko a cikin 1984, lokacin mulkin Buhari na soja, da aka shiga masifar tsadar rayuwa, kayan abinci sun yi tsadar da har kwanon wake ya kai naira 9. Na san mutane da yawa a ƙauyen mu da su ka kasa sayen wake su shuka. Saboda kuɗaɗen su duk sun salwanta wajen ruguguwar canjin sabbin kuɗi a lokacin. Inji Malam Auwalu.