Tiwita ya karyata wani sharhi da ake yadawa kan martani da wai yayi wa kalaman Buhari – Binciken DUBAWA

Zargi: Wani sharhi a shafin Tiwita da ake zargi ya fito daga kamfanin ya fayyace dalilan da ya sa kamfanin ya goge kalaman shugaba Muhammadu Buhari.

Ranar 1 ga watan Yuni 2021, Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya gana da shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman-kanta wato INEC, Mahmood Yakubu a fadar gwamnati, Abuja.

Yakubu ya gana da shugaban kasar ne dan kai rahoton jerin hare-haren da ake kaiwa a ofisoshin hukumar da ke jihohin kasar.

A martaninsa shugaba Buhari ya yi alkawarin cewa gwamnatinsa za ta baiwa INEC duk wani taimakon da take bukata dan shirye-shiryen zabukan da za ta gudanar a shekara ta 2023.

A sharhin da ya yi a shafin Tiwita bayan ganawar, shugaban ya yi kashedin cewa duk marasa kishin kasar da ke yayata tashin hankali da kuma ingiza mutane su kona kadarorin gwamnati a kasar za su gamu da abin mamaki.

Shugaban ya kuma kara da barazanar cewa zai murkushe duk wadanda ke kai hari kan ofisoshin INEC kamar yadda dakarun sojin kasar suka murkushe ‘yan tawaye lokacin yakin basasar Najeriya.

Buhari wanda janar ne mai ritaya, na daga cikin dakarun da suka kasance a filin daga lokacin yakin da ya yi sanadiyyar rayuka fiye da milliyan guda.

To sai dai bayanin da ya yi daga karshen gargadin na sa ya bata wa dimbin ‘yan Najeriya rai wadanda suka fassara furucin a matsayin wata barazana ga kabila daya a kasar.

Bayanin ya ce: “Da yawa daga cikin wadanda ke rashin hankalin yau, basu da wayon sanin irin lalata dukiya da kaddarori da ma rahsin rayukan da aka yi lokacin yakin basasar Najeriya. Mu da muka kasance a filin daga na tsawon watanni 30, mu da muka sha azabar yakin, za mu yi musu amfani da yaren da suka fi fahimta.”

‘Yan Najeriya da dama suka yi karar shafin shugaban kasar suna kira da a sanya wa shafin takunkumi, to amma maimakon sanya takunkumin sai dai tiwita goge bangaren sharhin da jama’a suka yi adawa da shi.

Kamfanin ya kuma yi tsokaci kamar haka, “Wannan sharhin ya karya dokokin Tiwita”

Wannan mataki da ta dauka ya fusata wasu daga cikin jami’an gwamnati musamman ministan watsa labarai da al’adu wanda ya yi Allah wadai da matakin a taron manema labaran da ya kira.

Hoton wani shafi da ake zargi na mahukunta Tiwita ne ya yi suna sosai a shafukan sadarwa musamman whatsapp, ya bayyana dokokin da shugaba Buhari ya karya wadanda kuma suka kai ga matakin soke sharhin na shi.

Bayanin da ake zargi ya fito daga mahukunta Tiwita cewa ya yi: @mBuhari ba mu san ko kai wane ne ba bare ma kasar da kake jagoranta, mun ga sharhin da ka yi a shafinmu amma ya karya dokarmu na hudu wanda ya danganci aminci da walwala, dan haka mun cire.”

Tantancewa

DUBAWA ta fara da duba shafin da kamfanin Tiwitan ke amfani da shi a hukumance wato @Twitter dan ganin ko ta wallafa wani abu mai kama da wannan amma ba ta ga komai haka ba. Sakamakon binciken dai ya kuma nuna cewa @Twitter bai wallafa wani abu a shafin shi bayan 28 ga watan Mayu 2021 ba yayin da kwanan watan da ke kan hoton da ake yadawa ke nuna 4 ga watan Yuni 2021 a matsayin ranar da kamfanin ya wallafa sakon.

Bayan haka, DUBAWA ta gano cewa an yi amfani da manhajan android ne wajen wallafa hoton sai dai kuma kowa ya san cewa @twitter yana amfani da manhajan sprinklr ko ta Twitter Web App ta wallafa sakonninta.

Haka nan kuma, Tiwita ba ta mayar da wani martani danagne da cire sharhin shugaban kasar da ta yi ba, tun bayan da abun ya faru.
DUBAWA ta gano cewa shafin Tiwitan shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana shi a matsayin shugaban kasar Najeirya. Daga lahadin da ya gabata shafin na aiki kuma akwai ma’abota milliyan 4.1.

Da DUBAWA ta yi amfani da dabaru na binciken kwa-kwaf a shafukan yanar gizo, ta gano cewa an kirkiro hoton ta amfani da dabaru na magudi. Da muka dauki hoton ya nuna mana inda aka kwaskware hoton alamar tiwitar da aka yi amfani da ita.

A karshe

Bincike ya nuna mana cewa hoton da ake yadawa ana zargin kamfanin tiwita da rubutawa na bogi ne. An yi amfani da dabarun fasaha ta zamani wajen hada hoton don yayi daidai da bukatun wadanda suka yi wannan abu.