TATTAUNAWA DA SARAKI:’Idan na zama shugaban ƙasa zan magance aringizon kuɗaɗen da ake yi wajen bayar da kwangiloli’

Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa kuma ɗaya daga cikin na sahun gaba a takarar shugabancin Najeriya a ƙarƙashin PDP, Bukola Saraki, ya bayyana cewa ɗaya daga garambawul da zai fara yi a ƙasar nan idan ya yi nasarar zama shugaban ƙasa, zai yi wa Hukumar Tantance Kuɗaɗen Kwangiloli (BPP) garambawul.
A cikin Tattaunawa ta Musamman da ya yi da PREMIUM TIMES, Saraki wanda ya yi Gwamna tsawon shekaru takwas a Jihar Kwara, kuma ya yi Shugaban Majalisar Dattawa daga 2015 zuwa 2019, ya ce kuɗaɗen yin kwangilar da ake yi a Najeriya sun yi yawan gaske.
Ya ce zai bada fifiko wajen ganin cewa an tabbatar da duk kwangilar da ya kamata a kashe naira biyar, “to Naira 5 ɗin za a kashe, ba Naira 25 ba.
“Saboda mutum zai yi mamakin irin maƙudan kuɗaɗe da ake kashewa a ƙasar nan wajen yin kwangiloli, amma kuma sai ka nemi ayyukan da aka na waɗannan maƙudan kuɗaɗe ka rasa.” Inji Saraki.
Da ya koma wajen inganta rayuwar al’umma kuwa, Saraki ya ce zai yi azamar ganin duk shekara ya gina gidaje 500,000 har tsawon shekaru huɗu na zangon sa na farko.
A batun samun kuɗaɗen shiga kuwa, Saraki ya tabbatar da wani kirdado da ya yi a cikin tattaunawar, inda ya ce kuɗaɗen da ke zurarewa ta hanyoyi daban-daban a ƙasar nan duk shekara, sun kai naira tiriliyan 8 zuwa 9.
Don haka ya ce zai yi ƙoƙari ya toshe waɗannan hanyoyin da kuɗaɗen ke zurarewa, domin Najeriya ta ƙara samun maƙudan kuɗaɗen shiga.
Ya yi maganar bijiro da hanyoyin da masu ƙananan ƙarfi za su riƙa samun halin gina gidaje, domin a cewar sa, mutanen da ke cunkushe su na rayuwa a ƙazaman matsugunai sun yi yawa a Najeriya.
Ya ce akwai ayyukan da Gwamnatin Tarayya ce ya kamata ta fitar da kuɗaɗe ta yi su ba.
“Wasu ayyukan kamfanoni masu zaman kan su ya kamata a bai wa su yi su. Amma akwai ayyukan musamman irin su bunƙasa wutar lantarki waɗanda ayyuka ne da gwamnatin tarayya za ta sa hannu ta yi da kan ta.” Inji Saraki.