TASHIN DUNIYAR MAI ƘARAR KWANA: Korona ta kashe mutum fiye da miliyan 1 cikin 2022, ta ci rayuka miliyan 6.4 daga 2020 zuwa yau -WHO

Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO), Tedros Ghebreyesus ya tabbatar da cewa ƙididdiga ta nuna korana ta kashe mutum fiye da miliysn 1 daga Janairu zuwa cikin Agusta, 2022, a wannan shekara kenan.

Cikin wani bayanin sa a ranar Alhamis, Tedros ya yi kira ga gwamnatocin ƙasashe su ƙara matsa ƙaimi wajen yi wa jama’a rigakafin korona.

“A wannan makon adadin waɗanda korona ta kashe cikin wannan shekarar sun haura miliyan ɗaya. Saboda haka ba za mu yi sakacin cewa wai yanzu mu na rayuwar sabo da korona har ta zama jiki ba, a wannan lokacin da cutar ta kashe mutum miliyan ɗaya a cikin watanni takwas ba.”

Tedros ya ce akwai buƙatar ci66 gaba da yin riga-kafi ta yadda za a samu yi wa aƙalla kashi 70 bisa 100 na duniya riga-kafi.”

Ƙididdigar Cibiyar Daƙile Cutar Korona ta Amirka a ranar 25 Ga Agusta, ta nuna cewa daga 2020 zuwa Agusta 2022, mutum miliyan 596.75 ne suka kamu da korona a duniya (596,759,069).

Haka kuma ƙididdigar dai ta tabbatar da mutuwar mutum miliyan 6.4 a duniya, daga 2020 zuwa Agusta 25 na watan da mu ke ciki (6,455,107).

Tuni dai a fadin duniya aka yi watsi da tsarin nesa-nesa da bayar da tazara a tsakanin jama’a. An daina amfani da matakan kariya. Kuma an koma ana cakuɗuwa a taron jama’a, kasuwanni da wuraren kallon wasa da wuraren holewa.