TALLE BAI YI WA AUDI GORI: Gwamna Wike ya ce Dino Melaye ba shi da natsuwa, kimtsi da kamun kan da zai riƙe muƙamin gwamna

Gwamna Nysome Wike na Jihar Ribas ya ce tunanin da Dino Melaye ke yi na zama gwamna a Jihar Kogi, abu ne da ba zai taɓa yiwuwa ba, saboda ba shi da kimtsi, natsuwa da kamun-kai da har za a amince a ba shi mulkin jiha sukutum.
Melaye wanda ya yi wa PDP Kakakin Yaɗa Labarai na Kamfen ɗin Zaɓen Shugaban Ƙasa, ya fara fafutikar neman zaɓen fidda-gwani na PDP a zaɓen gwamna da za a yi ranar 11 Ga Nuwamba a Kogi
Da ya ke magana cikin gungun ‘yan jarida ranar Talata a Patakwal, babban birnin Jihar Ribas, Wike ya ce ya na sane da irin ƙulle-ƙullen da PDP ke yi domin ta murɗe zaɓen fidda-gwani, ta bai wa Dino Melaye takarar gwamna a Kogi.
“Haba jama’a, Allah na tuba, ai Dino Melaye ba shi da kimtsuwa, kamun kai da natsuwar da zai zama gwamna kwata-kwata. Ai gwamna ba wasan kwaikwayo ba ne da zai fito a hasko shi a fim ko talbijin. Mu na da magana kan mulki ne, ba wasan kwaikwayo ba.” Inji Wike.
“Don me PDP ke shirin murɗe zaɓen fidda-gwani ta bai wa Dino Takara? Ai ta san dai idan ta bai wa Dino takarar gwamnan Kogi, to ta faɗi zaɓe kai-tsaye.
“Don me ‘yan Kogi za su ce za su zaɓi Dino? Me ya sa za mu maida gwamna kamar wasan ‘yan tashe ne?”
Wike ya ce idan PDP ta tsayar da Dino ɗan takarar gwamna a zaɓen Nuwamba, to idan an faɗi zaɓe kada wani maras kunya ya fito ya ce an yi wa PDP maguɗi, saboda dai tun farko PDP ba ta haɗa ƙwarya da abokin burmin ta ba.