SSS sun tsare Bawa bayan Tinubu ya dakatar da shi

A yanzu haka dai dakataccen Shugaban EFCC, Abdulrasheed Bawa ya kwana ofishin SSS, bayan amsa gayyatar da aka yi masa.
SSS sun gayyace shi jim kaɗan bayan sanar da dakatar da shi da Shugaba Bola Tinubu ya yi.
Kamun tsare Bawa ya zo ne kwanaki uku bayan SSS sun tsare Gwamnan Bankin Najeriya, Godwin Emefiele, wanda Tinubu ya dakatar a makon da ya gabata.
Gayyata da tsare Bawa na daga cikin binciken sa da aka fara, dangane da zargin sa da harƙalla, kamar yadda sanarwar dakatar da shi ta ƙunsa.
Kakakin SSS Peter Afunanya ne ya tabbatar da gayyatar da su ka yi wa Bawa da kuma tsare shin da aka yi, a sanarwar da ya fitar cikin shafin sa na Tiwita ƙarfe 10.48 na dare.
Dakatar da Bawa ya zo mako biyu bayan da aka samu rashin jituwa tsakanin EFCC da SSS a Legas, kwana ɗaya bayan rantsar da Tinubu.
Rikici tsakanin SSS da EFCC ya ɓarke ranar 30 Ga Mayu, yayin da SSS su ka tare duk wata hanya da EFCC za su bi su shiga ofishin su na Legas, har kusan tsawon yini ɗaya.
Sai da ta kai Shugaba Tinubu ya sa baki, kuma ya hore su su ka yin aiki kafaɗa da kafaɗa sannan lamarin ya saisaita.
PREMIUM TIMES ta buga labarin cewa Tinubu ya dakatar da Bawa daga EFCC.
Shugaba Bola Tinubu ya dakatar da Shugaban EFCC, Abdulrasheed Bawa ba tare da wani ɓata lokaci ba.
Cikin wata sanarwa da Daraktan Yaɗa Labarai na Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya, Willie Bassey ya fitar ba da daɗewa ba, an umarci Bawa ya gaggauta damƙa ragamar aiki a hannun Daraktan Ayyuka na EFCC.
Sanarwar ta ce an dakatar da Bawa har zuwa lokacin da za a kammala binciken zarge-zargen da ake yi masa.
Bawa wanda ya karɓi ragamar EFCC daga hannun Ibrahim Magu, shi ma ya yi irin fitar da Magu ya yi wa EFCC.
Tarihi ya nuna babu wani shugaban EFCC da ya taɓa kammala wa’adin sa ya sauka salum-alum, duk cire su aka riƙa yi.
An cire Nuhu Ribadu, haka ita ma Farida Waziri da Ibrahim Lamurde duk cire su aka yi.
Har yanzu dai ba a bayyana dalilin dakatar da Bawa ba, ko kuma takamaimen zargin harƙallar da ake yi masa.
Sai dai kuma idan ba a manta ba, tsohon Gwamnan Jihar Zamfara Bello Matawalle ya zarge shi da neman toshiyar baki ta dala miliyan biyu, zargin da EFCC tuni ta ƙaryata.
EFCC ta maida wa Matawalle raddi cewa ta na zargin sa da danne Naira biliyan 70 daga asusun gwamnatin Zamfara, shi ya sa ya ke ta borin-kunya.