Sojoji sun yi wujiwuji da tulin ƴan bindiga, sun kashe da dama sun kwato dabbobin sata

Sojojin Najeriya sun kawato sama da shanu 2,000 bayan bata kashi da suka yi da ‘yan bindiga a karamar hukumar Mariga a jihar Neja.
Maharan sama da 500 na hanyar shiga cikin ƙungurmin daji ne dake yankin Birnin Gwari, Jihar Kaduna da jihar Neja ne bisa babura inda sojoji suka buɗe musu wuta ta sama da kasa
Wani Dagace daga cikin kauyukan da maharan suka kai wa hari Adamu Warari ya ce maharan sun fi mutum 100 kuma sun kai wa masallatai da coci hari, gidajen mutane inda suka rika kashe maza, suna yi garkuwa da mata sannan suka saci shanu da dama kafin jami’an tsaro suka dira musu suka yi fatafata da su a hanya.
Warari ya c daga Birnin Gwari maharan sun biyo ta garuruwan Mariga, Kasuwan Garba, Kontagora, Kwimo sannan suka tsallako zuwa Magadan Daji, Yungo, Argida da Chubadi kyma duka a wadannan kauyuka sun sace wa mutane dabobi inda daga nan jami’an tsaro daga Bangi suka tare su a Kwimo.
Wata majiya mai tushe daga rundunar sojin Najeriya ta bayyana cewa sojojin sama da kasa ne suka tare maharan a Bangi kafin su koma inda suke zama a cikin daji kusa da Birnin Gwari.
Rundunar soji ta ce wasu dakarunta biyu sun ji rauni amma tuni har an kaisu asibiti a na basu magani.