Sojoji sun yi luguden wuta a dajin Zamfara, sun kashe sama da ƴan bindiga 45

Raba a Facebook

Tura zuwa Twitter

Jiragen saman rundinar sojin Najeriya sun hallaka gomman ƴan bindiga masu garkuwa da mutane a dajin Sububu dake jihar Zamfara.

PRNigeria ta ruwaito cewa an kashe shugabannin ƴan ta’addan na ƴan ciki da wajen  Najeriya a wani guri da ake tunanin gidan shugaban ƴan fashin ne Halilu Tubali a lokacin da suke tsaka da tattaunawa.

Wani babban jami’in leƙen asirin rundinar soji ya shaida wa PRNigeria cewa bayan samun labarin cewa manyan ƴan ta’addan za su yi taro a dajin na Sububu, sai suka yi gaggawan shirya kayan yaƙin jiragen sama domin far musu ta sama.

Ya ce a yayin farmakin an kashe manyan ƴan ta’addan har sama da mutum 45, kuma wani ɗaga cikin su da ya samu munanan raunuka ya tabbatar da haka.

Sai dai ya ce babu tabbacin ko shugaban ƴan ta’addan Halilu Tubali an kashe shi a yayin farmakin sojojin haɗin giwawar ta sama.