Shugaban Kasa Tinubu Ya Karrama ‘Yan Wasan Super Eagles Da Lambar Girmamawa Ta Kasa Ta (MON)

Washington DC — Shugaban Kasa Bola Tinubu ya karrama tawagar Super Eagles da lambar girmamawar ta kasa ta MON saboda bajintar da ta nuna a gasar cin kofin nahiyar afrika ta AFCON da aka kammala a baya-bayan nan a kasar Ivory Coast.

An kuma baiwa kowane daga cikin ‘yan wasan kyautar gida da fili a babban birnin tarayyar Najeriya, Abuja.

Najeriya ta zo a mataki na 2, inda tayi rashin nasara a hannun mai masaukin baki kasar Ivory Coast, wacce a karshe ta lashe gasar.

A talatar nan ne fadar Shugaban Najeriya ta karbi bakuncin tawagar ta Super Eagles inda ta karramasu da lambobin girmamawa.

Dukkanin mambobin da masu horas da kungiyar sun halara a liyafar ciki harda Alex Iwobi, wanda ya fuskanci tsangwama a yanar gizo saboda rashin nasarar tawagara hannun Ivory Coast.